Ana tuhumar Koroma mai shekaru 70 da laifuka hudu, ciki har da zargin hannu a yunkurin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin kasar a watan Nuwamba./Hoto:Getty

Tsohon shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya isa Nijeriya ranar Juma'a da maraice bayan wata kotun kasarsa ta amince ya tafi jinya.

Ranar Laraba ne kotun ta amince Koroma, wanda ya shugabanci Saliyo daga 2007 zuwa 2018, ya tafi Nijeriya domin yin jinyar wata uku.

Shugaban kasar Julius Maada Bio ya bayyana matakin kotun a matsayin "nuna jinkai" a yayin da ya yi jawabi da 'yan kasar ranar Alhamis da maraice.

Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan sha'anin tsaro Nuhu Ribadu da shugaban hukumar ECOWAS Omar Alieu Touray ne suka tarbi Koroma a filin jirgin sama da ke Abuja.

Tun da fari, mai bai wa Koroma, Sheriff Mahmud Ismail ya ce tsohon shugaban kasar na Saliyo ya shiga jirgin Saman Sojojin Nijeriya inda ya bar kasarsa ko da yake bai bayyana inda ya nufa ba.

Ana tuhumar Koroma mai shekaru 70 da laifuka hudu, ciki har da zargin hannu a yunkurin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin kasar a watan Nuwamba.

Ana fargaba cewa tuhumar da ake yi wa Koroma na da nasaba da tashin hankali da ya barke bayan zaben kasar na watan Yunin 2023 inda aka sake zaben shugaba Julius Maada Bio a wa'adi na biyu.

Babban dan takarar adawa a zaben ya ki amincewa da sakamakon zaben sannan wasu kasashen waje sun nuna shakku kan sakamakon zaben.

Dakile nasarar juyin mulki

Ranar 26 ga watan Nuwamba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a barikin soji da wani gidan yari da kuma wasu yankuna na kasar ta Saliyo, inda suka ‘yantar da fursunoni kusan 2,200 tare da kashe mutane sama da 20.

Bayan haka ne gwamnati ta ce juyin mulki ne da aka yi nasarar dakilewa wanda akasarin masu gadin Koroma suka jagoranta. An gayyaci tsohon shugaban kasar domin amsa tambayoyi a farkon watan Disamba.

Koroma ya yi Allah wadai da harin jim kadan bayan faruwar lamarin, kana lauyoyinsa sun kira tuhumar da ake yi masa da "zargi mara tushe kuma wani bangare na "bangar siyasa".

TRT Afrika