Tsohon Shugaban ƙasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya amince ya sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa duk da cewa wani hukuncin kotu na ɗaurin shekara 20 ya haramta masa tsayawa takara.
Gbagbo shi ne tsohon shugaban ƙasa na farko da aka soma yi wa shari’a a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya a Hague, sai dai daga baya an wanke shi daga zarge-zargen da ake yi masa a 2019.
“Ya amince ya tsaya wa Jam’iyyar PPA-CI“ (African People's Party-Ivory Coast) takara bayan wani taron kwamiti, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ta tabbatar.
Duk da cewa an wanke shi daga zarge-zargen da ake yi masa na take haƙƙin bil’adama a Hague, shekara guda kafin nan an yanke wa Gbagbo hukuncin ɗauri na shekara 20.
Gbagbo ya yi rashin nasara a zaɓen 2010 ga Alassane Ouattara, sai dai ya ƙi amincewa ya sauka wanda daga baya aka tayar da tarzoma inda har sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya suka shiga lamarin.
Shugaban ƙasa mai ci na yanzu Alassane Ouattara ya yi masa afuwa a 2022.
Jam’iyyar Mista Gbagbo ta ce za ta gudanar da babban taron jami’iyya domin sanar da Gbagbo a matsayin ɗan takara.
Haka kuma jam’iyyar ta ce za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin ganin cewa ta mayar da sunan Gbagbo a cikin na ƴan takara.
Hukuncin da aka yanke masa a 2018 ya raba shi da irin damar da yake da ita ta tsayawa takara.