Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon Firaministan Nijar Hama Amadou ya rasu.
Ɗan siyasar ya rasu a ranar Laraba yana da shekara 74 a babban asibitin Yamai da ke Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.
An haife shi a Youri a shekarar 1950 inda ya riƙe muhimman muƙamai a Nijar.
Ya riƙe muƙami na firaminista sau biyu daga 21 ga watan Fabrairun 1995 zuwa 27 ga Janairun 1996 a ƙarƙashin mulkin Mahamane Ousmane sai kuma ya ƙara riƙe wannan muƙamin tun daga 31 ga Disambar 1999 zuwa 7 ga Yunin 2007 a lokacin mulkin Mamadou Tanja.
A matsayinsa na shugaban gwamnati, ya sha gwagwarmaya wurin ganin an samu daidaituwar siyasa da kuma ɗora ƙasar bisa kyakyawan tsari.
Duk da haka bai tsaya nan a siyasa ba, inda a 2011 aka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisa, muƙamin da ya riƙe kenan har zuwa shekarar 2013.
Haka kuma a shekarar 2016, Hama Amadou wanda abokin hamayya ne na Jam’iyyar PNDS Tarayya, ya tsaya takarar shugaban ƙasar Nijar, inda ya kara da Mahamadou Issoufou sai dai bai samu nasara ba.
Haka kuma a 2021 ya nuna aniyarsa ta sake tsayawa takara sai dai fuskanci ƙalubale da dama da suka haɗa da batun shari’a wanda hakan ya hana shi tsayawa takarar.