Tsananin zafi ya daki wani ɓangare na ƙasashen Afirka a shekaru ukun da suka gabata, inda aka dinga samun mahaukaciyar guguwa, ambaliyar ruwa da fari waɗanda ke zama sanadin yunwa da rasa matsugunai. Suna haddasa mutuwa: ana fuskantar ɓullar cutar kwalara mafi muni a nahiyar.
A Kudanci da Gabashin Afirka, tun 2021 sama da mutane 6,000 ne suka rasa rayukansu, kusan 350,000 kuma suka kwanta rashin lafiya sakamakon cutar ta kwalara.
Malawi da Zambia sun fuskanci afkuwar kamuwa da kwalara mafi muni a tarihinsu. Zimbabwe ma ta sha fama sosai. Mozambique, Kenya, Ethiopia da Somalia ma sun fuskanci ɓullar cutar sosai.
Dukkan su sun fuskanci ambaliyar ruwa ko fari - a wasu lokutan ma dukka biyun - kuma mahukuntan kula da lafiya, masanan kimiyya da ƙungiyoyin bayar da agajin gaggawa sun ce fitar ƙwayoyin bakteriya daga ruwan da ke Afirka ne sabon misalin yadda zafi ya tsananta a nahiyar, wanda ke sanya cututtuka yaɗuwa.
"Kamuwa da cutar na ci gaba da daɗuwa sosai saboda matsalolin sauyin yanayi na ta mamaye ko'ina," in ji Tulio Oliveira, masanin kimiyya da ke Afirka ta Kudu wanda ke nazari kan cututtuka a ƙasashe masu tasowa.
"Talauci"
Oliveira, wanda ya jagoranci tawagar da ta gano sabon nau'in cutar korona a lokacin annobar Covid-19, ya ce samun ɓarkewar cutar a Kudancin Afirka na da nasaba da guguwa da ambaliyar ruwan da aka samu a yankin a ƙarshen 2021 da farkon 2022, inda hakan ya kai ƙwayoyin bakteriya zuwa ga yankunan da babu su.
Zimbabwe da Zambia sun fuskanci daɗuwar cutar a yayin da suke kuma fuskantar tsananin fari, kuma mutane sun dogara kan wuraren da ake samun ruwa da ba shi da tsafta sosai irin su rijiyoyin burtsatse, rijoyoyi marasa zurfi da tafkuna, wanda dukkan su na iya gurbata. Kwanaki kadan bayan afkuwar ambaliyar rwan da ta yi ajalin rayuka da yawa a Kenya da wasu sassan Gabashin Afirka a wannan watan, an samu ɓullar kwalara.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kira kwalara da sunan cutar talauci, a yayin da take yaɗuwa a yankunan da ba su da tsafta da fama da rashin tsaftataccen ruwan sha. A wannan shekarar Afirka ta fuskanci rasa rayuka ninki takwas sama da Gabas ta Tsakiya, yanki na biyu da ya fuskanci ibtila'in.
A tarihin rashin karfi da rauni, Afirka ta fi fuskantar hatsarin illolin sauyin yanayi da kuma tasirin El Nino, in ji kwararrun kula da lafiya.
A wani abu da ya zama aruwna dare, akwai karancin allurar riga-kafin cutar kwalara, wanda kasashen Afirka matalauta ke tsananin buƙata.
"Ba ta shafar ƙasashen da ke da arziki," in ji Der. Daniela Garone, jami'ar magunguna ta ƙasa da ƙasa ta Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka, wadda a Faransanci ake cewa MSF.
An zuba jarin biliyoyin daloli wajen yaƙi da wasu cututtukan da ke damun ƙasashe masu rauni a duniya, irin su cutar shan inna da tarin-fuka, yawanci saboda kasancewar waɗannan cututtuka na yaɗuwa kuma suna iya zamo wa annoba har ma a ƙasashe masu arziki. Amma ba haka abin yake da kwalara ba wadda ake iya shawo kan yaduwarta.
WHO sun ce a wannan watan akwai karanci sosai na riga-kafin digon baki na cutar kwalara a kasuwannin duniya. Tun farkon 2023, kasashe 25 - kadan da ke da bukatar gaggawa - sun nemi a ba su alluran miliyan 82 don yakar yaduwar cutar inda miliyan 46 kawai ake da shi.
Akwai sauran kwaya miliyan 3.2 da suka yi saura, wanda yana kasa da adadin miliyan biyar da ake son su zama a kasa a ajje. a yayin da a yanzu haka ake fuskantar annobar kwalara a Gabas ta Tsakiya, kasashen Amurka da Kudu Maso-Gabashin Asiya, Afirka ce ta fi illata da cutar.
Ƙarancin riga-kafi a duniya
Kungiyoyin GAVI da UNICEF sun bayyana cewa a watan da ya gabata an bayar da umarnin samar da alluran riga-kafin kwalara wanda zai karfafi rumbun alluran. Amma sakamakon karancin ya riga ya janyo asarar rayuka da dama.
Lilanda, wani gari da ke gefen Lusaka babban birnin Zambia, ya zama babbar cibiyar kwalara. Kududdifai na gangaroraw a kan tituna tsaftataccen ruwan sha ya zama kamar zinariya. A wannan waje, a cikin kwanaki biyu Mildred Banda ta shaida rasuwar ɗanta sakamakon kamuwa da kwalara, ta kuma garzaya asibiti don ƙoƙarin kuɓutar da rayuwar 'yarta matashiya.
Bai kamata kwalara ta dinga kashe kowa ba. Ana iya maganin cutar cikin sauki tare da riga-kafin ta a saukake - kuma alluran riga-kafinta ba su da wahalar samu.
Wannan bai taimaki dan Banda, Ndanji ba.
A lokacinda ya kwanta rashin lafiya saboda gudawa, an yi masa magani da ruwan gishiri da sukari a wani asibiti, kuma aka sallame shi. A wannan dare ne ruwan jikinsa ya sake ƙarewa.
"Ya kamata a ce tun da fari na gano yarona ba shi da lafiya," in ji ta, tana zaune a gidanta ɗan ƙarami. "Da ya kamata a ce na dauki mataki da sauri na mayar da shi asibiti. Ina ma dai na mayar da shi don kuɓutar da rayuwarsa."
Saboda ƙarancin allurar riga-kafin, Zambia ba ta iya gudanar da gangamin riga-kafi don yaki da cutar ba, bayan da ta barke a makociyarta Malawi. Ya kamata hakan ya zama kiran gargadi. Zambia ta bukaci taimakon gaggawa ne a lokacin da nata lamarin ya tabarbare.
A tsakiyar watan Janairu ne magungunan da ka iya kubutar da rayuwar Ndaji suka fara isa kasar. Ya rasu a ranar 6 ga Janairu.