TRT Afirka za ta bayar da labaran Afirka tsantsarta 

Kafar watsa labarai ta Turkiyya wato TRT ta kaddamar da sabon sashen Afirka da zai rika bayar da labarai a shafukan intanet.

Sashen zai kasance cikin harsuna hudu: Hausa da Swahili da Ingilishi da Faransanci.

Shugaban tashar TRT Mehmet Zahid Sobacı ne ya kaddamar da sabon sashen ranar Juma’a, yayin ‘Taron Koli na Watsa Labarai na Farko’ a birnin Istanbul, wanda TRT da Tarayyar Afirka kan Watsa Labarai suka shirya.

Sobaci ya ce kafafen watsa labaran Yammacin Duniya sun kwashe shekaru aru-aru suna bayar da labarai na rashin adalci game da nahiyar Afirka.

Ya kara da cewa sashen na TRT Afrika zai mayar da hankali ne wurin bayar da labaran "Afrika tsantsarta".

Hakan na nufin za a bai wa 'yan Afirka damar fadin labaransu yadda suke ba tare da kara musu gishiri na.

Sobaci ya ce za a rika yin labarai game da al'adun Afirka masu ban sha'awa da kirkire-kirkire da matasa da sauran lamura masu dadi da ba a cika ji ba daga Afirka.

"TRT Afrika za ta zama wani madubi da ke nuna irin manufofin Turkiyya" da kuma alakarta da Afirka, in ji shi.

TRT Afirka ta kunshi ma’aikata daga kasashe akalla 15 na nahiyar.

Hakan zai bayar da dama ta shiga lungu da sakon Afirka don zakulo labarai masu karfafa gwiwa da ilimantarwa.

Ayyukan TRT Afrika za su mayar da hankali a baki dayan nahiyar daga Gambiya zuwa Moroko daga Nijeriya zuwa Kamaru.

TRT Afrika