Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya nemi sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su mika mulki nan da wata tara kamar yadda Nijeriya ta yi a shekarun 1990.
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanya wa Nijar takunkumai bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.
Kazalika kungiyar ta yi barazanar yin amfani da karfin soji kan sojojin idan suka ki mayar da mulki hannun farar-hula.
Sojojin Nijar sun ce za su mika mulki nan da shekara uku kuma a ranar Alhamis sun umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar.
Labari mai alaka: Sojojin Nijar za su mika mulki nan da shekara uku: Janar Tchiani
Tinubu ya ce Nijeriya ta koma kan turbar dimokuradiyya a 1999 lokacin da tsohon shugaban kasar Janar Abdulsalami Abubakar ya mika mulki ga gwamnatin farar-hula.
Ba za a sassauta takunkumai ba
"Shugaban kasar bai ga dalilin da zai sa ba za a dauki irin wannan mataki a Nijar ba, idan har hukumomin sojin da gaske suke," a cewar wata sanarwa da kakakinsa ya fitar.
Kazalika sanarwar ta ce ba za a sassauta takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa Nijar ba har sai sojojin sun "dauki matakai da suka dace".
"Abin da sojojin suka yi ba wanda za a amince da shi ba ne. Da zarar sun sauya matsayarsu, mu ma za mu yi saurin cire takunkuman domin saukaka rayuwar 'yan Nijar," in ji sanarwar.