Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar da taron Majalisar Tattalin Arziƙin Nijeriya ya bayar na janye sabon ƙudurin haraji.
A yayin taron majalisar karo na 144 wanda mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima ya jagoranta, majalisar ta bayar da shawarar janye ƙudurin yi wa dokokin haraji garambawul daga gaban majalisar ƙasar.
Shawarar janyewar na zuwa ne bayan gwamnoni 19 na arewacin Nijeriya waɗanda suka taru a Kaduna a ranar Litinin tare da sarakunan gargajiya daga yankin sun tattauna tare da watsi da wannan kudirin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana akwai buƙatar majalisar tattalin arziƙin ta sha kuruminta, ta bari lamarin na haraji majalisar dokoki ta yi aiki a kansa.
“Shugaba Tinubu na jinjina ga mambobin Majalisar Tattalin Arziki musamman mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da gwamnoni 36 bisa shawarar su. Yana ganin shirin majalisa, wanda tuni aka fara, zai bayar da dama a samu gudunmawa da kuma sauye-sauyen da suka kamata ba tare da an janye kudirin ba daga majalisar tarayya,” in ji sanarwar.
“A yayin da ake buƙatar Majalisar Tattalin Arziki ta bari aikin ya ci gaba, Shugaba Tinubu yana maraba da tuntuɓa da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki tattaunawa kan duk wani lamari game da kudirin yayin da majalisar ke tunanin amincewa da shi.”
Haka kuma Shugaba Tinubun ya ce akwai yiwuwar a samu ƙarin shawarwari idan aka yi zaman jin ra’ayi na majalisa a game da wannan kudirin dokar harajin, inda ya ce kwamitin da aka kafa na gyaran dokokin harajin sai da ya yi tuntuɓa yadda ya kamata.
Wannan lamari dai ya jawo suka daga sassan ƙasar musamman arewacin ƙasar inda masana ke ganin sauya dokokin na haraji zai ƙara jefa jama’a a cikin matsi da mawuyacin hali.