Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya aike da tawagogi biyu zuwa kasashen Nijar da Libya da Algeria don warware rikicin siyasar da Jamhuriyar Nijar take ciki.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, wanda kuma shi ne jagoran kungiyar ECOWAS, ta ce an aika da tawagar farko Jamhuriyar Nijar.
Tawagar tana karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, da kuma shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS, Omar Alieu Touray.
Tawaga ta biyu kuwa ita ce ta mutum guda, Ambasada Babagana Kingibe, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, wanda zai ziyarci shugabannin Libya da Algeria don tattaunawa da su game da matsalar ta Nijar.
Sanarwar da Ajuri Ngelele, kakakin Tinubu ya sanya wa hannu, ta ambato shugaban na Nijeriya yana jaddada kira da a yi amfani da dabarun tattaunawa don warware badakalar da ta biyo bayan kifar da zababbiyar gwamnati a Nijar.
“Babbar damuwarmu ita ce dimokuradiyya da zaman lafiyar yankunan,” in ji Shugaba Tinubu, a yayin da yake magana bayan ganawa da tawagogin da za su tafi Nijar.
Wannan yunkuri na Shugaba Tinubu na zuwa ne kwanaki kadan bayan ECOWAS ta sha alwashin shawo kan rikicin Nijar, ciki har da yiwuwar amfani da karfin soji.
Shugaba Tinubu ya nemi duka wadanda abin ya shafa da su yi iya yinsu don kawo karshen rikicin cikin lumana za zummar tabbatar da zaman lafiya a fadin Afirka.
Tattaunawa
Tuni dai tawagar da Janar Abdulsalami Abubakar yake jagoranta ta isa birnin Yamai inda ta soma tattanawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.