Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya da su janye shirin zanga-zangar da suke niyyar yi a farkon watan Agusta mai kamawa.

Ministan Watsa Labarai na Nijeriya Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar gwamnati a Abuja bayan kammala ganawarsa da Shugaban Ƙasar, yana mai cewa Shugaba Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ita su jira su ga matakin da zai ɗauka a kan ƙorafe-ƙorafensu.

Roƙon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a fadin ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya jawo muhawara ta kowane ɓangare a ƙasar inda wasu ke goyon baya, wasu kuma suna kira da a guji yin “duk abin da ka iya sake taɓrɓarar da yanayin tsaro da dama ake ciki a ƙasar.”

Akwai rahotannin da ke zargin cewa hukumomin tsaro sun fara kama wasu da ake zargin su da hannu a kitsa zanga-zangar.

Minista Idris ya ce “Mun tattauna batun ƙasar gaba daya kuma Shugaban Ƙasa ya bukaci in sake sanar da ‘yan Nijeriya cewa yana sauraronsu, musamman ma matasa da ke kokarin yin zanga-zanga.

“Shugaban kasa ya ce yana sauraronsu kuma yana daukar abin da suke faɗa da muhimmanci; kuma yana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa kasar nan ta yi kyau ba don yau kadai ba har ma nan gaba.

“Kan batun zanga-zangar da aka shirya, Shugaban Ƙasa bai ga buƙatar hakan ba. Ya umarce su da su ajiye wannan tsarin. Ya buƙace su da su jira martanin gwamnati kan dukkan kokensu, ”in ji Ministan.

Atiku Abubakar

A nasa ɓangaren, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya ce dokar ƙasa ta bai wa ‘yan ƙasa damar yin zanga-zanga bisa kundin tsarin mulki.

“Bin diddigin wasu mutane da ake zargin su ne masu shirya zanga-zangar aiki ne na banza, tun da a bayyane yake cewa ‘yan Nijeriya, ciki har da magoya bayan Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki, suna cikin yunwa, da ɓacin rai, da rashin tudun dafawa a kan gazawa da rashin sanin makamar aiki na wannan gwamnati.”

Shirin zanga-zanga

An shafe kusan wata guda ana batun shirya zanga-zangar nuna adawa da matsin tattalin arziki da ke daɗa ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta, wacce ake son yin ta a duk fadin jihohin Nijeriya da babban birnin kasar Abuja a cikin watan Agusta.

Sai dai duk da yadda zanga-zangar ke jan hankali, ba a san su waye suke shirya ta “ta bayan fage ba.”

Ana ci gaba da samun hauhawar farashi musamman ta kayan abinci a Nijeriya, sai dai gwamnati tana ta bijiro da hanyoyin da ta ce na rage raɗaɗin da ake ji din ne, kamar irin rabon kayan abinci.

Sannan a makon da ya wuce gwamnatin tarayyar ta sanar da ƙarin mafi ƙrancin albashi zuwa Naira 70,000 daga Naira 30,000.

TRT Afrika