Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da Firaministan Indiya Narendra Modi a ranar Lahadi sun tattauna kan batun hadin gwiwa ta ɓangaren yaƙi da ta’addanci da tsaron cikin teku da kuma sanar da juna bayanan sirri.
Shugabannin biyu sun gudanar da wannan tattaunawa ne a fadar shugaban Nijeriya da ke Abuja, kamar yadda mai magana da yawun shugaban Nijeriya Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
A daidai lokacin da ake samun ƙaruwar barazana a mashigar Tekun Guinea da Tekun Indiya, shugabannin biyu sun yi magana kan ɗaukar matakai na haɗin gwiwa domin kawo tsaro a cikin tekunan da kuma yaƙi da ‘yan fashin teku.
Modi ya yi wa Nijeriya alƙawarin taimaka wa ƙasar kawo ci gaba a ɓangaren tsaro, inda ya bayyana cewa Indiya ƙasa ce “amintacciya wurin samar da kayayyakin tsaro.”
An kammala tattaunawar ne da saka hannu kan yarjejeniyar wadda ta mayar da hankali kan batun shirye-shirye na musamman na al’adu da ƙara haɓaka dangantaka tsakanin ƙasashen ta ɓangarori da dama.
Firaministan na Indiya ya isa Nijeriya ne a ranar Asabar inda ya samu kyakkyawar tarba daga tawaga ta musamman ta shugaban Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja Nyesom Wike.
An gudanar da wani ƙwarya-ƙwaryar fareti ga Mista Modi a Fadar Shugaban Nijeriya kafin soma tattaunawa a tsakaninsu.
Haka kuma Shugaban na Nijeriya ya karrama Mista Modi da lambar yabo ta GCON.