ECOWAS da wasu kasashen Yamma sun saka takunkumi kan sojojin da ke mulki a Nijar bayan sun hambarar da Bazoum. Hoto/OTHER

Tawagar Malaman addinin Musulunci na Nijeriya ta isa Yamai babban birnin Nijar don ganawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Tawagar, wadda ke karkashin jagorancin shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta je kasar ne don neman mafita game da rikicin siyasar kasar bayan sojojin sun ki amincewa su mayar da shugaban kasar kan mulki.

Sabon Firaiministan kasar Ali Mahaman Lamine Zeine ne ya tarbi tawagar a filin jirgin saman Diori Hamani, a cewar kamfanin dillancin labarai na Nijar ANP press agency.

Malaman sun je Nijar ne kwanaki kadan bayan sun gana da shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS a fadarsa da ke Abuja.

"Yanzu haka tawagar Malaman tana Yamai bayan ta samu amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu don ta kashe wutar rikicin da ta tashi a Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi har ya sa ECOWAS ke shirin amfani da karfi a kansu," in ji wata majiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito ranar Asabar.

Likita ya gana da Bazoum

A bangare guda, a karon farko sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bayar da dama likita ya gana da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito daya daga cikin mutanen da likitan ya tafi da su yana cewa likitan ya kai wa shugaban da iyalansa wadanda suke tsare tare abinci.

Hakan na faruwa ne kwana guda bayan sakataren harkokin wajen Amurka ya ce sojojin da suka yi juyin mulkin sun ki sakin iyalan Bazoum.

Dama dai Bazoum ya yi korafin cewa busashiyar shinkafa da taliya sojojin suke ba shi.

A Lahadin da ta gabata ne dai wa’adin da ECOWAS ta bai wa sojojin kasar na su mika mulki ga farar hula ya kawo karshe, wanda bayan hakan ne ECOWAS din ta bukaci dakarunta da su daura damarar yaki.

AFP