A yanzu haka Amurka na da sama da soji 1,000 a Nijar. / Hoto: Others

Wata tawagar gwamnatin Amurka ta kai ziyara Nijar a ranar Talata domin tattaunawa da sojojin da ke mulki a ƙasar, kamar yadda kafar talabijin ɗin gwamnatin ƙasar ta sanar.

Gidan talabijin na ƙasar Tele Sahel ya bayyana cewa tawagar Amurka daga ciki har da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Molly Phee sun tattauna da firaiministan na Nijar a Yamai.

A ranar Talata, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce Janar Michael Langley wanda shi ne kwamandan sojin Amurka da ke kula da sojojin ƙasar da ke Afirka, na daga cikin tawagar da ta kai ziyara Nijar.

Ana kallon wannan tattaunawar kamar yunƙurin sasanci ne tsakanin Amurka da Nijar bayan sojojin ƙasar sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum inda suka ƙara matsawa kusa da Rasha.

A wata taƙaitacciyar sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen ta ce tawagar Amurkan za ta tattauna da sojojin na Nijar kan “mayar da Nijar kan turbar dimokuraɗiyya da kuma makomar ci gaban tsaro da haɗin kai a tsakanin ƙasashen.”

Har yanzu Amurka na da sojoji kimanin 1,000 na Nijar a wani sansani da ta gina na jirage marasa matuƙa a sahara inda ta kashe dala miliyan 100 – sai dai an taƙaita zirga-zirga tun bayan juyin mulkin inda Amurkar kuma ta dakatar da bayar da taimako ga gwamnatin ta Nijar.

Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya kai wata ziyara wadda ba a saba ganin irinta ba a Nijar a shekarar da ta gabata a lokacin da Mohamed Bazoum ke kan mulki a yunƙurin kawar da masu iƙirarin jihadi.

Sai dai bayan wata huɗu, sojojin sun kifar da gwamnatin Bazoum inda suka yi masa ɗaurin talala.

Sojojin da ke mulkin na Nijar sun raba gari da Faransa wadda ita ce ta yi musu mulkin mallaka, lamarin da ya sa Faransar ta janye sojojinta da ke a Nijar ɗin tsawon kusan shekara goma.

Sai dai sojojin na Nijar ɗin waɗanda suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa da na Amurka ba su buƙaci na Amurkar su fice daga ƙasar ba.

AFP