Wata tawaga daga kungiyar ECOWAS ta bar Nijar ba tare da ganawa da jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a kasar ba, kamar yadda wani mamba a tawagar ya bayyana.
Tawagar ta isa birnin Yamai a ranar Alhamis "sai dai ba ta kwana ba" kamar yadda aka tsara, kuma ba ta gana da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tchiani ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani mamba a tawagar yana cewa.
Kazalika ba ta hadu da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.
Tsohon Shugaban Nijeriya Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci tawagar kuma an tsara za ta gana da Tchiani don gabatar masa da bukatar kungiyar ECOWAS, kamar yadda fadar shugaban Nijeriya ta bayyana.
Nijeriya ce ke kan kujerar shugabancin kungiyar ECOWAS a halin yanzu kuma ta sanya takunkumi a kan sojojin Nijar sannan ta ba su wa'adin mako daya su dawo da Bazoum kan mulki.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ECOWAS za ta yi bakin kokarinta wajen warware matsalar cikin ruwan sanyi amma za ta iya amfani da karfin soji a matsayin mataki na karshe.
Sai dai jagoran juyin mulkin Nijar ya yi gargadi cewa a shirye suke mu mayar da martani mai karfe.
"Duk wata barazana ko wani yankuri a kan Nijar, to Rundunar Sojin Nijar za ta mayar da martani nan take ba tare da sanarwa ba kan daya daga cikin mambobin kasashen ECOWAS," in ji daya daga cikin wadanda suka jagoranci juyin mulkin a wata sanarwa da ya karanta a gidan talabijin ranar Alhamis.
Sojojin sun soke jerin kawancen soji da ke tsakanin kasarsu da Faransa a wani mataki da ake gani zai yi tasiri sosai a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.
Kazalika sun janye jakadun Jamhuriyar Nijar daga Faransa da Amurka da Nijeriya da kuma Togo.
Hambararren shugaban kasar ya ce sojojin da suka tumbuke shi daga mulki suna garkuwa da shi, kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen dawo da gwamnatin farar-hula kan mulki.
A wata makala da ya wallafa a jaridar The Washington Post, Bazoum ya yi kira ga "Amurka da dukkan kasashen duniya su taimaka mana domin dawo da tsarin mulki."
"Sojojin da suka kitsa juyin mulki sun yi karya cewa sun dauki matakin ne domin kare tsaron Nijar. Sun yi zargin cewa yakin da muke yi da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi ya gaza kuma tsare-tsarena na tattalin arziki da walwalar jama'a, ciki har da hada gwiwa da Amura da Turai, suna cutar kasarmu," in ji Bazoum.
Sai dai ya ce ya inganta rayuwar 'yan Nijar da sanya kasar a kan turba mai kyawu.
"A hakikanin gaskiya, tsaron Nijar ya yi matukar inganta — sakamakon hada gwiwar da muke yi wacce sojojin ke adawa da ita. Yanzu tallafin da muke samu daga kasashen waje shi ne kashi 40 na kasafin kudinmu, amma hakan ba zai dore ba idan juyin mulkin ya yi nasara," a cewar Mohamed Bazoum.