Kusan bayan shekara daya bayan da Rasha ta kaddamar da “aikin soji na musamman” a Yukren ranar 24 ga watan Fabrairun bara, ana jin karar tafiyar takalman sojoji da tankokin yaki a nahiyar Afirka.
Yakin ya faru a wani lokacin mara kyau ga nahiya ta biyu mafi yawan mutane a duniya, wadda take fama da matsalar tattalin arziki da kuma tabarbarewar zamantakewa da cutar korona ta janyo.
Yakin bai nuna wata alamar karewa ba. Haka kuma matsalolin tattalin arzikin Afirka mai rauni – wanda ya dogara kan hatsi da kuma makamashin da ake shigowa da su.
Tashin gauron zabin da farashin iskar gas da man fetur suka yi saboda yakin ya sa farashin sauran abubuwa ya karu, lamarin da ke nuna cewa matsalar tattalin arzikin ka iya ci gaba da damun ‘yan Afirka tsawon lokaci.
Matsalar ta ta’azzara
Uganda na daya daga cikin kasashen Afirka da dama da suke shan wahala har yanzu saboda tasirin rikicin, wanda ya barke wata daya kacal bayan da kasar ta sake bude tattalin arzikinta bayan shafe tsawon watanni yana kulle saboda cutar korona.
Abin da rikicin ya fara shafa shi ne farashin mai – litar man fetur daya wadda ake sayarwa kan dalar Amurka 1.2 ta koma dala biyu daga tsakanin watan Maris zuwa watan Disamban shekarar 2022.
Duk da cewar farashin mai ya sauka kadan zuwa dala 1.5 a kowace lita, har yanzu ‘yan Ugandan na jin radadin tasirin hakan.
Uganda ba ta kayyade iya kudin da za a sayar da kayayyaki kamar Kenya ko Rwanda ba, saboda tsarinta na jari hujja.
Saboda haka gwamnatin kasar ba ta iya sa baki cikin maganar farashin man fetur ba. Wannan tsarin na sakar wa mutane mara ya kuma hana boyewa da kuma tsadar mai.
Wasu ‘yan siyasa a Afirka sun alakanta wahalar da ‘yan nahiyar ke sha da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha.
A Kenya, yakin da ake yi a Yukrain ya kawo tsaiko ga shiga da fitar da kayayyakin saye da sayarwa bayan an kakaba wa Rasha takunkumi.
Wannan ya sa farashin mai ya karu sosai, lamarin da ya yi tasiri kan farashin abinci da kuma sauran kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.
Hana fitar da kayayyaki waje, wanda ya kai na kudi dala miliyan 7.5 a kowace shekara, ya biyo bayan dakatar da dakon kayayyaki na wucin gadi daga shigarwa da kuma fitarwa cikin Rasha da kamfanonin dakon kaya suka yi, a wani mataki na mayar da martani kan takunkumin da aka kakaba wa Rashar.
Kusan wata biyu bayan an fara rikicin Yukren, Kenya ta fuskanci wani tsadar man fetur din da ba ta taba gani ba. Rikicin ya sa an rufe wasu gidajen mai. Bayan haka farashin kayayyakin abinci ya karu matuka.
A watan Yuni, masana’antun sun yi korafi kan tsadar dala. An alakanta matsalar rashin kudi a hannun jama’a da yakin da ake yi din wanda ya dora wa asusun kudaden kasashen wajen kasar nauyi mai yawa.
Dogaro da kai kan samar da abinci
Nahiyar Afirka, kamar yawancin sauran sassan duniya, ta dogara ne kan Rasha da Yukren wajen samun alkama.
Rikicin Yukrain da kuma takunkumin da aka kakaba wa Rasha sun katse hanyar tafiyar da kaya, lamarin da ya janyo rikici mai tsanani a kasashe da dama.
Kenya – wadda take sayen kashi 30 cikin 100 na alkamar da take bukata daga Rasha da Yukren – ta fuskanci tsananin tsada don boye kayayyakin abincin da ake yi.
Mafi yawan kasashen Afirka sun dogara ne kan alkamar da ake shigar da ita.
Kasashen Kamaru da Djibouti da Burundi da Togo da Senegal da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Tanzaniya da Rwanda da Togo da Libiya da Mauritaniya da kuma Namibiya, suna shigar da kashi 50 zuwa 70 cikin 100 na alkamarsu.
Yayin da Madagaska da Masar suke amfani da kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na alkamar da ake shiga da ita. Somaliya na shiga da kashi 90 cikin 100 alkamarta.
Eritrea ce kasar da matsalar ta fi shafa saboda tana shiga da dukkan alkamarta daga Yukrain da Rasha.
Sai dai kuma Eritrea daya ce daga cikin kasashe biyar da suka ki amincewa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na Allah-wadai da yunkurin Shugaba Vladamir Putin na kwace larduna hudu daga Yukrain.
Habasha ba ta kada kuri’a ba a majalisar. Washe garin ranar Firaminista Abiy Ahmed ya ce rikice-rikicen cikin kasarsa sun nuna karara yadda yaki ka iya saka al’ummomi da iyalai da hanyoyin samu da kuma tattalin arziki cikin matsala.
“A yayin da za yi tunanin cewar za a iya saurin cike gurbin tasirin yaki, tasirinsa a kan al’umma na iya zama tabo ga kasashe,” in ji Abiy.
Dogaro da kai a harkar abinci abu ne muhimmi ga kasashen Afirka, kuma matsalar tsadar da yakin ya haifar ta kasance babbar matsala ga kasashen da ke fama da fari da sauyin yanayi da rikici da kuma matsalolin da annobar cutar korona suka janyo.
“A yayin da za yi tunanin cewar za a iya saurin cike gurbin tasirin yaki, tasirinsa a kan al’umma na iya zama tabo ga kasashe."
A yayin da yawancin kasashen Afirka suka dogara kan harkar noma, yakin Yukren ya yi tasiri kan shigar da taki daga Rasha.
Ghana, tana shigar da kashi 50 cikin 100 na takinta daga Rasha ne.
Diflomasiyya mai tsare rayuka
A shekarar da ta gabata, hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ta bayar da taimakon abinci da agajin jin kai ga yawancin kasashen da lamarin ya shafa.
Wannan ya biyo bayan kyakkyyawar diflomasiyyar Turkiye ta hanyar samar da hatsi, inda ta sa Rasha da Yukrain suka rattaba hannu kan yarjejeniyar taimaka wa sama da mutum miliyan biyu a Habasha, wadanda suke fama da tsananin yunwa a ranar 22 ga watan Yulin bara.
Madalla da shiga tsakani na diflomasiyya da Turkiye ta yi, wanda ya jawo hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta samar da tan 23,000 na hatsi ga Habasha.
Hakazalika, ta hanyar shirinsu na magance yunwa a Afirka, kungiyoyin ba da agaji na Red Cross da Red Crescent sun taimaki wasu kasashen nahiyar da matsalar ta shafa sosai, inda Senegal ta kasance daya daga cikinsu.
Senegal tana shigar da sama da kashi 50 cikin 100 na hatsin da take bukata daga Yukren da Rasha.
Wannan yakin, ya nuna muhimmancin karfafa tattalin arzikin Afirka maimakon mayar da hankali kacokan kan harkokin tsaro kawai.
Lokaci ya yi da masu rike da madafun iko a Afirka za su farfado da kungiyoyin hadin gwiwa kamar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Gabas da ire-irensu, don samun ci gaba mai dorewa da kuma hadewar tattalin arzikinsu.
Ana ci gaba da yakin da ake yi a Yukren har yanzu, kuma tsadar rayuwa a kasashen Afirka har yanzu ba ta sauko ba. Wannan zai ci gaba da tasiri a kan ci gaban kasashe da yawa a nahiyar.