Polling unit in Equitorial Guinea/ AA

Daga Alphonce Shiundu

A kowane lokaci idan aka samu al'umma mai yawan matasan da ke amfani da shafukan sada zumunta kuma suke samun labarai ta wajen, to akwai barazanar yaduwar labaran karya da farfaganda.

Irin wadannan labarai kan gurbata sahihan bayanan da ke yaduwa a fadin duniya, musamman ma a lokutan zabuka.

Ya zama tamkar jiki a harkokin yau da kullum yadda masu mu’amala da shafukan sada zumunta ke amfani da dabarun yada labaran karya don bata abokan hamayya a idon al'umma.

Sukan kuma lalata bayanan da suka shafi muhimman al'amura, kuma Afirka ma ba ta tsira daga irin wannan ta'asa ba.

Irin wadannan al'amura na karuwa sosai a lokutan zabuka daban-daban, a matsayin wasu makaman fafutukar yakin neman zabe.

Miliyoyin 'yan Nijeriya ne daga cikin miliyan 96 da suka yi rijistar zabe suka fita kada kuria'a a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, don zabar sabon shugaban kasa, a zaben da aka mayar da hankali kansa sosai a nahiyar Afirka a bana.

Shafukan sada zumunta a Nijeriya na kan sharafi da tashe ta yadda suke da matukar tasiri a al'amura daban-daban.

Rahotanni na nuna yadda masu fada a ji a shafukan ke jan ra'ayin matasa masu zabe wajen yakin neman zabe.

Baya ga Nijeriya, akwai wasu kasashe hudu na Afirka da su ma za su yi zabe a wannan shekarar.

Saliyo za ta yi nata a watan Yuni, a watan Yuli ko Agusta kuma Zimbabwe za ta yi nata zaben, sai Laberiya a Oktoba sai kuma a watan Disamba za a yi a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

Dukkan wadannan kasashe biyar suna da miliyoyin matasa kuma da yawan matasan suna amfani da shafukan sada zumunta.

Miliyoyin 'yan Nijeriya ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Fabrairun 2023/Photo AA

Sai dai hakan na zuwa da karuwar yada labaran karya da sauran kalubale da ke shafar yada labarai. To amma me ya kamata kasashen su yi don kare yanayin siyasarsu daga barazanar labaran karya da ke bata ruwa?

Ga wasu darussa 10 da za su iya koya daga kasar Kenya:

1. Fahimtar 'yan baranda:

Su waye mutanen da ke yada labaran karya? Dan siyasa daya suke zaba su yi wa wannan aiki ko kuwa suna iya yi wa kowa ma musamman wanda ya fi ba su kudi, wato iya kudinka iya shagalinka?

Mene ne ke tunzura su yin hakan? Suna aiki tare ne don yada labarai da zantukan karya ga mutane a kan batutuwan siyasa ko kuwa a karan kansu kawai suke wannan aiki?

Yin kyakkyawan nazari kan batun da ya fi tashe a shafukan sada zumunta da kuma amfani da dabarun leken asiri a shafukan ka iya taimakawa wajen gano baragurbin da ke yada labaran kanzon kurege da suka shafi siyasa.

2. Tsara abin da zai yi tashe ko jan hankali:

Wadanne irin batutuwa suke tsarawa, kuma da wadanne kafafe suke amfani? Hotuna da zane-zane kawai suke amfani da su wajen yada labaran karyar ko kuwa har bidiyo ma ana amfani da shi ta hanyar sauya shi da siddabaru?

Ana yada karerayin a bayyane karara a Twitter da Tiktok da Facebook da Instagram ne ko kuwa cikin sirri ake kitsawa da watsa su a WhatsApp da Telegram?

Yin sharhi kan batun da ke raba kawunan jama'a, da maudu'an da ke tashe za su iya tsarge irin salon da ake bi wajen tsara su da kuma sanin dabarun irin martanin da ke biyo baya.

3. Dakile karerayi:

Idan har ana son dakile bazuwar labaran karya, to dole a kambama sahihan bayanan da ke tattare da muhimman batutuwa.

Alal misali, tuni wata kungiya mai bin diddigin labaran karya ta Africa Check mai cibiya a Nijeriya ta samar da wani shafin intanet da nan da nan za a iya duba bayanan gaskiya da suka danganci zabukan kasar.

Bayanan da ake dubawa sun hada da yadda jam'iyyu ke samun kudaden kamfe har ma da kuri'ar jin ra'ayin jama'a. Kungiyar Africa Check ta yi irin wannan aiki a lokacin zabukan kasar Kenya.

4. Hadin kai don tattara sahihan bayanai:

Ana sa ran kafafen yada labarai da 'yan jarida da masu bin diddigin labaran karya za su tattara sahihan bayanan da za su taimaka wa mutane yanke hukuncin da ya dace a kan zabukan.

A Kenya an samar da wani shiri na hadin gwiwa a fannin yada labarai mai suna Fumbua; ita ma Nijeriya tana da wata gamayya ta masu bin diddigin gano gaskiyar labarai.

Yin aiki tare don yaki da labaran karya a zamanin siyasa na taimakawa wajen dakile duk wani kokari na yada labaran kanzon kurege a kowane mataki, da hana bazuwarsa da kuma samar da sahihan bayanai.

Baya ga Nijeriya da aka yi zabe akwai wasu kasashen Afirkan ciki har da Laberiya da za a yi zabe a 2023/Photo AA

5. Tattaunawa:

A mafi yawan lokuta labaran karya na siyasa da ake yadawa kan raba kawunan jama'a, kuma idan ba a yi taka-tsantsan ba hakan zai iya tayar da rigima.

Sai dai akwai abubuwan da za a iya yi da za su taimaka wajen samar da yanayi na lumana a tsarin, kamar shirya tattaunawa kan batutuwan da aka samu mabambantan ra'ayoyi a kansu, da kuma shigar manyan mutane harkokin yakin neman zabe, ciki har da 'yan takara.

6. Kamfanonin sada zumunta:

Kamfanonin shafukan sada zumunta suna da tsare-tsare da muradunsu ta fuskar kasuwanci da al'amuran yau da kullum.

Ya kamata kungiyoyin fararen hula su kulla abota da wadannan kamfanoni don su dinga ankarar da su kan duk wasu bayanai masu hatsari da suke yaduwa kamar wutar daji a kasashen da hakan ke faruwa don kare tsarin dimokradiyyarsu.

A nasu bangaren, su ma masu amfani da shafukan soshiyal midiya ya dace su dinga kai korafi ga kamfanonin a duk lokacin da suka ci karo da wani abu da ya saba dokokin dandalin.

Bugu da kari idan suka ga wata kullalliyar manufa daga wasu shafuka to akwai bukatar sanar da kamfanonin don a katse su.

A karshe kuma ya kamata duk kamfanin shafin sada zumuntar da ba shi da isassun dokoki na tsare bayanan da ke yaduwa, to ya kamata a ankarar da shi da matsa lamba har sai ya samar da tsarin.

7. Wayar da kai:

Ya zama wajibi kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula su dinga bibiya da wayar da kan masu ruwa da tsaki a harkar yada bayanai don tabbatar da cewa an samar da ingantacce da sahihin tsari wajen bayyana ra'ayoyi da muhawara.

Ya kamata kungiyoyin fararen hula su kulla abota da kamfanonin soshiyal midiya don ankarar da su kan bayanai masu hatsari da ke yaduwa kamar wutar daji /Photo Reuters 

Su kuma dinga tattara bayanai na labaran karya da ake yadawa a lokutan kamfe tare da fallasa masu yada labaran kanzon kuregen.

Akwai kuma bukatar su dinga wayar da kan mutane a zamanance kan intanet don ilimintar da masu kada kuri'a yadda za su iya gane labaran karya da kuma hana yada su.

8. Saurin yaduwa:

Karya ta fi gaskiya da sahihan bayanai saurin yaduwa kamar wutar daji. Yana da muhimmanci kwarai a dinga bin diddigi tare da gano gaskiyar labaran bogi a lokutan zabuka da zarar sun fara yaduwa a kafafen sada zumunta.

Gaggauta gano gaskiyar labari da yadawa na dakile bazuwar labaran bogi masu alaka da siyasa. Babu amfanin yin hakan bayan kammala zabe, zai zama tamkar ihu ne bayan hari.

9. Yin bakam:

A wasu lokutan ana shirya labaran karya na siyasa ne da gangan don abokan hamayya da kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula su mayar da martani ko su dauki mataki.

Yawanci ana hakan ne don a janyo zazzafar muhawara kan wasu batutuwa masu sarkakiya saboda kawai a shigar da su cikin al'amuran yau da kullum.

Bin diddigin abin da lamarin ya kunsa da bincike kan labaran karya na siyasar a tsanake kafin yin martani, kan taimaka kwarai.

Wasu labaran karyar ma ana iya kin mayar da hankali a kansu ko kuma a dauki matakin ba tare da kambama su a yadda suka zo ba.

10. Taba kimar hukumomi:

Ana yawan kokarin taba martabar hukumomin zabe masu zaman kansu a wadannan kasashe.

Irin wannan lamari na rage kima da yardar da mutane suka yi wa masu kula da hukumomin zaben, inda a karshe sai a dinga dari-dari kan yiwuwar samun sahihin zabe marar magudi.

Abin da zai taimaka wajen hana wannan yunkuri tasiri shi ne, hukumomin su samar da sahihan hanyoyi na kare kansu da suka hada da bin diddigi da binciken gaskiyar labaran karyar da ake yadawa da kuma karyata su da hujjoji.

Duk da cewa darussan da za a koya din suna da yawan da ba za a iya zayyano su gaba daya ba, wadannan goman da aka fada za su taimaka kwarai wajen rage yada labaran karya na siyasa.

Za kuma su samar da ingantaccen tsari a dimkoradiyya ta yadda masu zabe za su iya daukar hukunci a karan kansu ba tare da gurbata musu tunani ba.

Alphonce Shiundu shi ne editan kungiyar Africa Check a Kenya, kuma mataimakin shugaban Fumbua, wani shiri na hadin kai na aikin jarida da aka kirkira don yaki da labaran karya a Kenya.

TRT Afrika