Kungiyar AU ta samu nasarori da dama tsawon shekara 24 da kafa ta. Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Shekara 24 da suka gabata – a ranar 9 ga watan Satumbar 1999 – shugabannin Afirka sun taru a birnin Sirte na Libiya domin wani muhimmin lamari a tarihin nahiyar, wanda aka kafa wani ginishiki na cimma muradu a tare.

Zuwa lokacin, kungiyar Organization of African Union wato OAU ita ce ke hada kan nahiyar wadda ke da bambancin kasa da jama’a da siyasa da al’adu.

Taron na Sirte shi ne ginshikin abin da duniya ta sani a yau a matsayin Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) - kungiyar da aka kaddamar a hukumance a shekarar 2002 don maye gurbin OAU a matsayin babban hadin kai tsakanin kasashen Afirka da jama'arsu.

Sakamakon taron na Sirte, sai aka amince kan cewa nahiyar na bukatar sabuwar kungiya wadda ta dace domin ta tunkari irin kalubalan da ake fuskanta a lokacin, daga ciki har da cika burin wasu daga cikin kasashen da ba sa karkashin mulkin mallaka kai tsaye.

Wani abu kuma da shugabannin Afirka suke son gani a lokacin shi ne kara habaka siyasa da zamantakewar al’umma a nahiyar.

Tafiya ta yi tafiya

Duk da cewa AU tana tafiya kan tafarkin da wadanda suka kirkiro ta suka dora ta a kai kusan shekara 25 da suka gabata, amma masu sharhi na ganin har yanzu akwai sauran aiki a gabanta.

Daya daga cikin matakan da AU ta dauka shi ne tabbatar da cewa akasarin kasashen Afirka sun saka hannu kan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge a 2018.

Babban dalilin wannan yarjejeniyar ita ce alkawarin cire miliyoyin mutanen Afirka daga talauci da kuma kara fadada kudin shiga da dala miliyan 571, kamar yadda wani bincike da Bankin Duniya ya yi ya bayyana.

Haka kuma binciken ya nuna cewa kasashen Afirka sun fi cinikayya tsakaninsu da na sauran kasashen duniya fiye da yadda suke yi a tsakaninsu.

Masu sharhi sun bayar da misali da irin wadannan bayanan kan cewa akwai bukatar kungiyar ta AU din ta kara bayar da himma ta bangarori da dama.

“Gaskiyar magana ita ce ba mu samu wani ci gaban da muke so mu samu ba,” kamar yadda Mahmud Jega ya bayyana wa TRT Afirka, wanda shahararren dan jarida ne na Nijeriya.

“Muna sa ran Afirka za ta yi kama da Kungiyar Tarayyar Afirka zuwa yanzu – hade kan tattalin arziki watakila da kudi na bai daya; watakila da fasfo daya ta yadda shige da fice tsakanin kasashen ba zai zamo ana bukatar biza ba, da sauran hanyoyin hadin kai,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa duk da wasu sassa na nahiyar kamar Yammacin Afirka da Kudancin Afirka sun yi kokari wurin hade kan yankunan, babu wasu shawarwari masu yawa da za a bayar.

“Zuwa wani mataki yankin kasashen Larabawa na Afirka ya yi kokari wurin hadin kai. Amma hadin kan yankin baki daya? A gaskiya har yanzu akwai sauran aiki a gaba,” in ji Jega.

Farfesa Kamilu Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano na da irin wannan ra’ayin na Jega.

“A lokacin da OAU ta koma AU, an ta sa rai kan cewa AU din za ta ci nasara a tarihi fiye da OAU, musamman kan batun hadin kan Afirka,” in ji shi.

“Yadda aka tsara lamarin shi ne an so AU ta kasance kamar yadda Tarayyar Turai take. Sai dai bayan waccan yarjejeniyar ta siyasa, ba ta dage wurin hadin kan jama’a kamar yadda mutane suka yi zato ba,” in ji shi.

Juyin mulki da rashin zaman lafiya

An yi ta ambaton nahiyar a ‘yan kwanakin nan a labarun duniya sakamakon yadda ake ta juyin mulki a wasu kasashe da kuma rashin zaman lafiya, inda aka samu yunkurin juyin mulki da juyin mulkin kusan sau 10 a nahiyar tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu.

A daidai lokacin da wannan guguwar ta juyin mulki ke kara bazuwa, masu sa ido a Gabon na ganin cewa akwai bukatar a kara bayar da himma domin dakile sauyin gwamnatin da ake yi ba tare da bin ka’idar kundin tsarin mulki ba.

“Yadda AU za ta dakile juyin mulki da kuma tabbatar da zaman lafiya a nahiyar ne babban kalubale a yau,” kamar yadda Jega ya bayyana.

“An yi juyin mulki da dama – a Guninea da Mali da Burkina Faso da Nijar da Sudan yanzu kuma a Gabon – wata alama ce ta damuwa wadda ke da alaka da wasu matsalolin.

"Wadannan sun hada da matsalolin tattalin arziki da yadda talauci yake a nahiyar da kuma gaskiyar cewa dimokuradiyya ba ta kama nahiyar yadda ya kamata ba.”

Jega ya yi bayani kan cewa dimokuradiyya ta wuce batun gudanar da zabe lokaci bayan lokaci a kasashe da dama na Afirka.

“Kusan duka kasashen da ake gudanar da zabe – ko dai Kenya ko Saliyo ko Nijar ko Gabon – akwai zarge-zarge na magudi da rashawa da watsi da ra’ayin al’umma, da sauransu,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Cire wa’adi da wasu zababbun ‘yan siyasa ke yi a Afirka wata alama ce ta watsi da ra’ayoyin jama’a, lamarin da masu sa ido ke ganin ya kamata AU ta yi tsaye a kai.

Farfesa Fagge ya bayyana cewa akwai bukatar AU ta yi amfani da diflomasiyya wurin magana ga duk wani shugaba ko na farar hula ko koma bayan hakan wanda yake da akidu da ke barazana ga dimokuradiyya.

“Ina tunanin akwai bukatar AU ta kalli wannan bangaren domin ganin idan mu ‘yan Afirka na kokarin kula da dimokuradiyya. Duk wanda ya saba mata ta hanyar sauya kundin tsarin mulki ko kuma tsawaita wa’adi ko rashin hakuri da ‘yan adawa – duka wadannan barazana ce ga dimokuradiyya.”

Rashin zaman lafiya a wasu kasashe na Afirka na daga cikin wasu kalubalen da masu sharhi ke ganin ya sa akwai bukatar AU ta magance wadannan matsalolin.

“Lamari mafi muni da muke da shi a halin yanzu shi ne Sudan inda lamarin ke tafiya kamar irin na Somaliya, inda ake rikici tsakanin bangarorin soji biyu tsawon sama da watanni uku inda dubban mutane ke mutuwa, hakika wannan babbar matsala ce ,” in ji Jega.

Tasirin kasashen Yamma

Duk da cewa rusashiyar kungiyar OAU ta taka muhimmiyar rawa wurin ceto kasashen Afirka da dama daga mulkin mallaka, sai dai yadda kasashen na Yamma ke ci gaba da katsalandan a nahiyar na ci gaba da karuwa.

A ‘yan kwanakin nan, an ta samun sha’awa da nuna ra’ayi daga kasashen Yamma a Afirka inda suke son a ba su dama musamman ta tattalin arziki.

Masu sharhi na ganin cewa akwai bukatar a yi amfani da hankali wurin mu’amula da harkokin kasashen waje, inda wasu ke ganin hada kai wurin ciniki ita ce kadai hanyar da Afirka za ta bi wurin samun riba a mu’amularsu da kasashen Yamma.

“Duk da cewa Afirka baki dayanta tana cin gashin kanta gomman shekaru, amma muna shan wahala wurin kawar da matsalolin da Turawan mulkin mallaka suka dasa mana, musamman yadda suka tsara dangantakar kasuwanci tsakanin kasashenmu da na su,” in ji Jega.

Yana ganin cewa idan dai har nahiyar ta ci gaba da fannin tattalin arziki, to za ta iya sallama da dangantaka irin ta mulkin mallaka na zamani da kashen Yamma suka gina bayan sun tafi.

Shi ma Farfesa Fagge ya yarda da hakan inda yake cewa akwai bukatar nahiyar ta kara dogara da kanta.

“Mu daina dogara da wasu kasashe domin magance matsalolinmu. Mu yi da kanmu. Idan za su zo wurinmu, su zo su taimaka – ba wai su ba mu umarni kamar shugaba ba,” in ji shi.

A daidai lokain da AU ta ke kara wasu shekaru, tunani kan abin da zai iya kasancewa a bayyane yake tare da fatan Afirka za ta kara samun ci gaba.

TRT Afrika