Taron Commonwealth: An nemi Birtaniya ta ɗauki batun biyan diyyar bauta da muhimmanci

Taron Commonwealth: An nemi Birtaniya ta ɗauki batun biyan diyyar bauta da muhimmanci

Firaministan Bahamas Philip Davis ya nemi Biritaniya da ta yi la'akari da ta'addancin da aka yi lokacin cinikin bayi.
Nigerian security forces have been fighting against Boko Haram and other armed groups for more than a decade. Photo: Reuters

Firaministan Bahamas, Philip Davis, ya ce yana son tattaunawa ta gaskiya da takwaransa na Birtaniya Keir Starmer a taron ƙasashen renon Ingila da ake yi a Samoa game da lamarin nan mai sarkakiya na biyan diyya game da zakuncin da aka aikata a lokacin mulkin mallaka.

Wannan na zuwa ne bayan batun da Starmer ya yi a ranar Litinin kan cewa Birtaniya ba za ta taso da wannan batun ba a yayin taron.

Davis a ranar Alhamis ya bayyana cewa zai buƙaci shugabanni su tattauna batun nan biyan bashi kan cinikin bayi a taron ƙungiyar ƙasashen renon Ingila ta Commonwealth.

Sarkin Birtaniya Charles III ya amince da kiraye-kirayen da wasu daga cikin tsoffin yankunan Birtaniya suka yi wa mulkin mallaka na a yi la'akari da rawar da ta taka a cinikin bayi na tekun Atlantika.

Gidan Sarautar Birtaniya ya fahimci cewa "lamari mai raɗaɗi na abubuwan da suka gabace mu na ci gaba da bayyana," kamar yadda ya shaida wa shugabanni a Apia a ranar Juma'a.

Sai dai sarkin bai yi magana a kan batun diyyar da za a biya ba ga ƙasashen, kamar yadda shugabannin duniya suka buƙata.

Sai dai sarkin ya buƙace su da su samu "kalamai masu kyau" da kuma fahimtar tarihi "tare da ɗora mu a kan hanya wurin ɗaukar matakin da ya dace a nan gaba a wuraren da ke fama da rashin daidaito."

Tattaunawar da aka kasa kammalawa

"Babu wani a cikinmu da zai iya sauya abin da ya faru a baya, amma za mu iya amfani da zukatanmu mu koyi darasi da kuma neman hanyoyi ta yadda za a gyara rashin daidaiton da aka samu," kamar yadda Sarki Charles ya bayyana, wanda yake halartar taron ƙungiyar ƙasashen renon Ingila a karo na farko a matsayinsa na shugaban gwamnatin Birtaniya.

Kalaman nasa a wurin bikin bude taron a hukumance sun yi daidai da kalaman kwana daya da farko da Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya yi cewa taron ya kamata a kauce wa shiga tsakani a baya da kuma "tattaunawa mai tsawo mara iyaka game da ramuwa."

Shugaban na Birtaniya ya yi watsi da kiraye-kirayen da kasashen Caribbean suka yi wa shugabanni a bikin na shekara-shekara da su tattauna karara kan gyara rawar da Birtaniyya ke takawa a cinikin bayi tare da ambaton lamarin a cikin sanarwar hadin gwiwa ta karshe.

Sai dai yadda Birtaniyya ke tafiyar da harkokinta a cinikin bayi da ke ratsa Tekun Atlantika, masu lura da al'amura da dama na ganin tamkar wani babban gwaji ne na yadda kungiyar Commonwealth ta daidaita da duniyar yau, kamar yadda sauran kasashen Turai da wasu cibiyoyi na Birtaniyya suka fara daukar nauyin rawar da suke takawa a cinikin.

"Ina tsammanin lokaci ya yi da za a dauki wannan da muhimmanci," in ji Jacqueline McKenzie, abokiyar tarayya a kamfanin lauyoyi na London Leigh Day. "Babu wanda ke tsammanin mutane za su biya kowane dinari guda don abin da ya faru. Amma ina ganin akwai bukatar a yi shawarwari."

Daga karni na 15 zuwa na 19, akalla 'yan Afirka miliyan 12.5 ne jiragen ruwa da 'yan kasuwa na Turai suka yi garkuwa da su tare da kai su Turai da ƙarfin tsiya, aka sayar da su a matsayin bayi.

Waɗanda suka tsira daga mummunan bulaguron sun ƙare sun yi aiki a gonaki a ƙarƙashin yanayin rashin mutuntaka a cikin Amurka, galibi a Brazil da Caribbean, yayin da bayinsu suka ci gajiyar aikinsu.

TRT Afrika da abokan hulda