Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfin soji idan sojojin ba su mayar da mulkin kasar hannun farar hula ba./ Hoto: AFP

Kungiyar Tarayyar Turai ta dauki matakin shari’a domin kakaba takunkumi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Tarayyar ta Turai mai kasashe 27 ta yi Allah wadai da hambarar da gwamnatin zababben shugaban Nijar Mohamed Bazoum.

Tarayyar Turan ta dauki matakai na shari’a inda a halin yanzu za ta iya saka “takunkumi kan jama’a ko kamfanoni wadanda suke da alhakin kawo barazana ga tsaro ko zaman lafiya kan Nijar,” kamar yadda ta bayyana a ranar Litinin.

Shugaban tsare-tsaren harkokin waje na tarayyar ya bayyana cewa wannan matakin “zai aika sako cewa akwai matakin da ke biyo bayan juyin mulkin soji.

Tuni Tarayyar Turai ta dakatar da hadin kan tsaro da kuma tallafin kudi ga Nijar bayan sojoji sun kwace mulkin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Daina bayar da tallafi

“Matakan da aka dauka sun hada da kwace kadarori da kuma hana bayar da kudi ga jama’a da kuma kamfanoni, da kuma haramta tafiye-tafiye ga jama’a,” kamar yadda Turai ta ce a wata sanarwa.

Kasar da ta yi wa Nijar mulkin-mallaka wato Faransa a halin yanzu tana janye dakarunta 1,500 daga kasar bayan sojojin na Nijar sun bukaci hakan.

Labari mai alaka: Amurka za ta bai wa Mohamed Bazoum taimako 'mara iyaka'

Kasashen Yamma na kallon hambarar da Bazoum a matsayin wani babban koma- baya a yakin da suke yi da ta’addanci a yankin Sahel saboda ana kallon Bazoum a matsayin babban mai bayar da gudunmawa.

Kungiyar ECOWAS ta saka takunkumi kan kasar a daidai lokacin da ake juyin mulki a yankin na Sahel. Sai dai a halin yanzu tana bin hanyoyin diflomasiyya domin magance lamarin.

TRT Afrika da abokan hulda