Akalla mutane uku ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wasu hare-haren bam biyu da aka kai a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.
Bama-baman da suka tashi a yammacin ranar Asabar, an dasa su ne a kan babbar hanyar da ke tsakanin gundumar Dharkinley da Kahda a kudu maso gabashin Mogadishu, hanyar da jama'ar yankin ke yawan amfani da ita.
Wani jami'in tsaro a Mogadishu ya ce, bisa sharadin sakaya sunansa saboda takunkumin da aka sa na magana da kafofin watsa labarai, ya ce akwai yiwuwar adadin waɗanda suka rasu ya iya ƙaruwa idan aka yi la'akari da yawan mutanen da ke amfani da hanyar da maraice.
Ya ce jami’an tsaro sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka killace hanyar domin daƙile cunkoson ababen hawa tare da gudanar da bincike.
Babbar barazana
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai tagwayen hare-haren, amma kungiyar ta'addanci ta Al Shabab mai alaka da Al Qaeda ta dauki alhakin kai irin wadannan hare-hare a babban birnin kasar a baya bayan nan.
Kasar Somaliya dai ta shafe shekaru tana fama da matsalar rashin tsaro, inda babbar barazanar ke fitowa daga kungiyar Al Shabab da kuma kungiyoyin ta'addancin Daesh.
Tun a shekara ta 2007, Al Shabab ke yakar gwamnatin Somaliya da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Somaliya (ATMIS) - wadda tawaga ce mai sassa daban-daban wadda Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ba amince da ita da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Kungiyar ta'addancin dai ta kara kai hare-hare tun bayan da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud ya ayyana "babban yaƙi" kan kungiyar.