Dubban 'yan kasashen waje da 'yan Sudan na cigaba da ficewa daga kasar a yayin da rikicin ya shiga mako na uku . (KARIM SAHIB / AFP)

Ana jin karar hare-haren jiragen sama da makamai da ke kakkabo jirage da igwa a Khartoum a yayin da aka shiga mako na uku na rikicin da ake yi tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun Rapid Response Force.

Ana cigaba da rikici tsakanin bangarorin biyu duk da yarjejeniyar da suka kulla ta tsawaita tsagaita wuta ranar Juma'a inda ake ta jin harbe-harbe da fashewar abubuwa a Khartoum da biranen Bahri da Ombdurman.

Daruruwan mutane sun mutu yayin da dubbai suka jikkata sannan wasu dubban suke cigaba da tserewa daga kasar a yayin da da ake gwabza fada tsakanin sojin kasar da dakarun RSF, tun bayan barkewar rikici ranar 15 ga watan Afrilu.

Rikicin ya kawo tsaiko ga shirin da ake yi na mayar da kasar turbar dimokuradiyya.

"Babu wani amfanin neman mulki a kasar da take wargajewa," in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a hirarsa da gidan talbijin na Al Arabiya.

Fadan ya tado da tsohon yakin da aka kwashe shekaru aru-aru a lardin Darfur inda a makon jiya aka kashe mutane da dama.

Rundunar soji ta rika amfani da jirage da jirage marasa matuka tana kai hari a yankin da ke hannun mayakan RSF a babban birnin kasar. Fadan ya jefa 'yan kasar cikin garari inda suke fada da karancin abinci da ruwa da hasken lantarki.

Bayanai sun nuna cewa an kashe fiye da mutane 500 tun da rikicin ya barke tsakanin dakarun da ke karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da na RSF da ke karkashin jagorancin mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Burhan da Daglo sun amince da yarjeniyoyin tsagaita wuta sau da dama sai dai ba sa mutunta ta lamarin da ya ta'azzara yakin sannan ya yi sanadin mutuwar karin mutane.

Dubban 'yan kasashen waje suna cigaba da ficewa daga kasar a yayin da kasashen duniya ke cigaba da kira da a shawo kan rikicin.

Reuters