Wasu mazauna yankin Omdurman a yayin da suke karɓar tallafin abinci / Hoto: Reuters Archive

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya [WFP] ya yi gargaɗi game da mummunan yanayin da ake ciki a Sudan, yana mai cewa ƙasar tana dab da faɗawa "bala'in yunwa mafi girma a duniya".

Leni Kinzli, mai magana da yawun WFP a Sudan, ranar Juma'a ta gudanar da taron manema labarai ta manhajar bidiyo inda ta yi gargaɗi cewa "lokaci yana ƙurewa a yunƙurin hana faɗawa cikin bala'in yunwa" da watsuwar yaƙi a yankin El Fasher sakamakon rashin samun damar shigar da kayan agajin jinƙai.

"Shekara guda da aka kwashe ana yin wannan mummunan rikici a Sudan ta haifar da babban bala'i lamarin da ke barazanar haddasa masifar yunwa mafi girma a duniya," in ji ta, inda ta ƙara da cewa ba a iya kai tallafin abincin da ya kamata a lardunan El Fasher da Darfur saboda "faɗan da ake yi tare da matsalolin da suke da nasaba da tsare-tsare."

Kinzli ta ce suna ƙoƙarin kai tallafi ga mutum kimanin 700,000 kafin damuna ta sauka, a yanzu da ake iya bin hanyoyi kuma suna da tan kimanin 8,000 na abinci da ke ajiye a Chadi, amma suna fuskantar ƙalubale wurin isar da waɗannan kayayyakin abinci.

WFP ta yi kiran gaggawa wajen samun tabbacin tsaron lafiyar ma'aikatanta kafin ta soma shigar da kayan abinci ƙasar, tana mai cewa rikicin da ake yi a El Fasher ya sa tuni kimanin mutum miliyan 1.7 suka faɗa cikin yunwa.

Kinzli ta ƙara da cewa kusan mutum miliyan 28 a Sudan da Sudan ta Kudu suna fuskantar yunwa, inda ta yi kira ga ƙasashen duniya su sanya hannu don kai musu ɗauki.

Kazalika ta tunatar da ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan cewa ya zama wajibi su kiyaye dokokin ƙasashen duniya game da jinƙai.

Sojojin Sudan ne suke da iko a lardin El Fasher, kuma suna samun goyon baya daga ƙungiyoyin sa-kai waɗanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba a 2020.

An kashe dubban mutane, an raba miliyoyi daga muhallansu

Yaƙin Sudan ya ɓarke ne ranar 15 ga watan Afrilun 2023 sakamakon saɓanin da aka samu tsakanin shugaban rundunar sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al Burhan da tsohon mataimakinsa kuma shugaban rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces [RSF] Mohamed Hamdan Dagalo.

Alƙaluma sun nuna cewa yaƙin ya yi sanadin mutuwa fiye da mutum 16,000 sannan an raba kusan mutum miliyan biyu da muhallansu, inda suka tsare zuwa maƙwabtan ƙasashe irin su Chadi, Masar, Ethiopia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Kusan mutum miliyan 8.5 ne suke gudun hijira a cikin ƙasar.

Har yanzu an kasa yin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu duk da shiga tsakanin da Saudiyya da Amurka suka kwashe tsawom lokaci suna yi.

TRT World