Mahamat Idriss Deby, ya karɓi mulki jim kaɗan bayan kisan mahaifinsa. Hoto: Getty Images

Gwamnatin soji ta riƙon ƙwarya a Chadi ta amince da bai wa jagoran hamayya izinin koma wa gida, wanda ya tsere daga ƙasar bayan wani mummunan hari da aka kai kan masu zanga-zangar neman a yi gaggawar miƙa mulki ga gwamnatin dimokuradiyya, kamar yadda Ƙungiyar Ƙasashen Yakin Tsakiyar Afirka ECCAS ta rawaito a ranar Talata.

Succes Masra ya tsere daga Chadi ne bayan da aka kashe gomman mutane tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da dakarun tsaro suka far wa masu zanga-zanga a babban birnin ƙasar N'Djamena a ranar 20 ga watan Oktoban 2022.

Bayan ya tsere ne sai gwamnati ta sanar da neman a kama shi da taimakon ƙasa da ƙasa.

Amma Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Felix Tshisekedi, wanda Ƙungiyar ECCAS ta naɗa a matsayin mai shiga tsakani a batun komawar Chadi turbar dimokuraɗiyya, ya sanya hannu kan wata sanarwa da ke cewa gwamnatin sojin Chadin da jagoran hamayya Masra sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a ranar Talata.

Yarjejeniyar za ta bai wa Masra da duk sauran mutanen da suka bar ƙasar bayan abubuwan da suka faru ranar 20 ga watan Oktoban 2022 ɗin damar koma wa gida, ECCAS ta faɗa a sanarwar.

Tun watan Afrilun shekarar 2021 Chadi ke cikin rigingimu bayan mutuwar Shugaba Idriss Deby, wanda ya mulki ƙasar tsawon shekara 30.

Ɗansa Mahamat Idriss Deby, ya ƙwace mulki jim kaɗan bayan kisan mahaifin nasa, kuma da fari ya yi alkawarin jagorantar ƙasar tsawon wata 18 ne kacal sai a yi zaɓuka.

Amma a farkon watan Oktoban bara sai ya sanar da cewa zai ƙara shekara biyu, lamarin da ya jawo mummunar zanga-zanga.

Reuters