Rundunar Sojin Sudan SAF ta ce ta amince ta yi zaman sulhu da dakarun RSF cikin wannan mako a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
Matakin na zuwa ne bayan da tawagar SAF ta janye daga tattaunawar a watan Yuli wadda Amurka da Saudiyya suka dauki nauyin shiga tsakani.
Mataimakin kwamandan Rundunar sojin Sudan Laftanar Janar Shams Aldin Alkabashi, ya ce sojojin sun samu goron gayyata a hukumance daga masu shiga tsakani, ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da tattaunawar a ranar Alhamis.
“Tattaunawar za ta fara ne da batutuwan da suka shafi jilkai, ciki har da kai agaji a yankunan da ake yaki.
Sannan rukuni na biyu a tattaunawar zai kunshi hanyoyin tsagaita wuta, sai kuma mataki na karshe da zai shafi tsarin siyasa da kokarin kawo karshen yakin kasar,” in ji shi.
Tasirin lamarin ga dubban mutane
Dubban mutane ne aka kashe yayin da wasu dabban suka jikkata tun bayan barkewar yakin Sudan a ranar 15 ga watan Afrilun bana tsakanin SAF da RSF.
Laftanar-Janar Shams al-Din al-Kabashi ya sake bayyana bayan dogon lokacin da ya kwashe ba a ji duriyarsa ba.
Kabashi, wanda aka ajiye a babban kwamandan rundunar SAF da ke babban birnin kasar Khartoum, ya bayyana a garin Wadi Sayyidna da ke arewacin kasar a ranar Asabar.
A watan da ya gabata ne, kwamandan dakarun hammaya ta RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, ya ce a shirye tawagarsa take domin zaman sulhu don kawo karshen rikicin da ya barke a watan Afrilu.
Ba a yi nasara ba wajen cimma a mastaya ta zaman sulhu a baya ba sakamakon rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangorin biyu da ke fada da juna suka ki cimma.