Wani babban janar na sojin Sudan ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa na tura kayayyaki ga rundunar RSF, inda ya fito fili ya caccaki kasar kan katsalandan a yakin da sojin kasar ke yi da RSF.
Wannan ne karo na farko da sojojin suka kama sunan wata kasa, duk da yake a baya sun bayyana cewa akwai kasashen makwabta da ke katsalandan a wannan yakin, wanda ya raba sama da mutum miliyan shida da muhallansu tare da jawo kashe-kashen kabilanci a Darfur.
“Muna da bayanan sirri na soji da kuma bangaren diflomasiyya da ke nuna cewa Hadaddiyar Daular Larabawa tana tura jirage domin bayar da agaji ga Janjaweed,” kamar yadda Janar Yassir al-Atta ya bayyana a wani jawabi ga mambobin Hukumar Leken Asiri ta Masar a Omdurman, a wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta.
Rundunar RSF ta samo asali ne daga mayakan Larabawa na Janjaweed wadanda suka taimaka wa sojojin Sudan suka dakile juyin-juya hali a shekarun 2000.
Da yake mayar da martani kan wannan zargin, wani jami'in Hadaddiyar Daular Larabawa, ya ce tun farkon yakin, Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi ta kira akai-akai kan a sassauta rikicin, da tsagaita bude wuta, da fara tattaunawar diflomasiyya a Sudan.
Ya kuma ce daular ta bayar da tallafin kayan agaji domin rage matsalolin jinkai a Sudan da kasashen da ke makwabtaka, daga cikin agajin har da kafa wani asibiti na wucin gadi a birnin Amdjarass a watan Yuli, kamar yadda jami’in ya bayyana.
Janar Atta ya kuma yi zargin cewa Hadaddiyar Daular Larabawan ta kuma bayar da kayayyaki wadanda ba a san iyakarsu ba ga RSF ta Uganda da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Chadi.
Ya kuma bayyana cewa ko a wannan makon sai da kayan agajin suka iso ta filin jirgin Ndjamena babban birnin Chadi bayan a baya an samu wasu kayan ta Amdjarass, in ji shi.
Haka kuma Janar din ya jinjina wa Rasha na tarwatsa rundunar Wagner wadda ya zarga da taimakawa wurin shigar da kayayyakin ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.