Sojojin Sudan da dakarun rundunar Rapid Response Force, RSF, sun sake amincewa su tsagaita wuta ta awa 72 ranar Lahadi duk da yake a baya ba su yi biyayya ga yarjeniyoyin tsagaita wutar da suka kulla ba.
Rundunar sojin kasa ta Sudan ta ce za a soma aiki da tsagaita wutar ne da misalin karfe goma na dare a agogon GMT, tana mai cewa sun amince da matakin ne bayan "Amurka da Saudiyya sun shiga tsakani".
Ita ma rundunar RSF ta tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.
"Mun sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 72 sakamakon shiga tsakani na kasashen duniya da na yankunanmu, inda za ta soma aiki da tsakar daren yau. Hakan zai bayar da dama ga masu aikin jin kai su samu damar kwashe mutane sannan jama'a su samu damar biyan bukatunsu da kai wa yankunan da ke da tsaro," a cewar sanarwar da RSF ta fitar.
An kashe akalla mutum 528 yayin da aka jikkata fiye da mutum 4,000 tun da fadan ya barke ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin rundunar soji da ke karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun RSF da ke karkashin Janar Mohammed Dagalo.
Ganau sun ce an cigaba da musayar wuta ranar Lahadi inda jiragen yaki suka rika rugugi a Khartoum, babban birnin kasar da Omduran mai makwabtaka.
Hukumar kula da sararin samaniyar ta sanar ranar Lahadi cewa samaniyar Sudan zai cigaba da kasancewa a rufe zuw ranar 13 ga watan Mayu, ko da yake za a rika barin jiragen da ke kai kayan agaji da masu kwashe jama'a su sauka.
"Ana ta ba-ta-kashi da jin karar harbe-harbe," a cewar wani mazaunin kudancin Khartoum a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.