Sojojin sun jaddada cewa Nijeriya ta fi dacewa da mulkin dimokuradiyya./Hoto: Reuters

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta yi watsi da masu kira ga sojojin kasar su yi katsalandan a tsarin dimokuradiyya.

A wata sanarwa da hedikwatar ta fitar a ranar Asabar, ta ce sojojin kasar sun nuna rashin jin dadinsu game da wani labari da ake watsawa a intanet cewa ba sa jin dadi da walwalwa a kasar.

Sanarwar ta ce shugaban sojin kasar Janar CG Musa ya jaddada biyayyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana mai cewa ba zai kauce wa aikinsa da kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tsara ba.

“Kiraye-kirayen da ake yi ga sojoji su yi katsalandan a dimokuradiyya rashin kishin kasa ne da mugunta da kuma yunkurin kawar da hankalin sojojin Nijeriya daga gudanar da ayyukansu da kundin tsarin mulki ya tsara,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ta kara da cewa dakarun sojin Nijeriya ba za su tsoma baki kan duk wani batu da zai yi zagon-kasa ga dimokuradiyya ba.

“A yayin da rundunar sojin Nijeriya ta mayar da hankali wurin kyautata wa dakarunta, muna kyamar duk wani yunkuri na wani ko wata kungiya da za su harzuka sojojin Nijeriya masu bin doka domin su sauya gwamnati a kasarmu.

“Muna so mu bayyana karara cewa sojoji suna farin ciki sannan sun fi dacewa a karkashin mulkin dimokuradiyya kuma ba za su shiga duk wani aiki na zagon-kasa ga dimokuradiyyar da aka samu a kasarmu ba,” in ji sanarwar.

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta fitar da wannan sanarwa ce a yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bukaci dakarunta su daura damarar yaki da sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar.

TRT Afrika