Yawan satar man fetur da fasa bututun mai, yana janyo cikas ga Nijeriya. Hoto / Reuters / File

Sojojin Nijeriya sun lalata akalla haramtattun wuraren tace ɗanyen fetur 27 tare da kwace ɗanyen mai na sata, biyo bayan farmakin da suka kai a cikin makon nan a wuraren da ake haƙar mai a Kogin Delta da ke yankin yankin Neja, kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana a ranar Laraba.

Yawan satar man fetur da fasa bututun mai, yana janyo cikas ga Nijeriya, kasar da ke kan gaba wajen samar da makamashi a nahiyar Afirka.

Kazalika hakan na gurgunta harkokin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya gurgunta kudaden gwamnati inda hakan ya zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Shugaba Bola Tinubu yake fuskanta.

Mukaddashin mai magana da yawun rundunar Danjuma Jonah Danjuma ya ce an kama kusan lita 100,000 ta danyen sata a yayin samamen.

An kuma kama wasu motoci uku maƙil da tataccen mai ba bisa ka'ida ba.

Wannan samame na daga cikin ayyukan da ake ci gaba da yi na dakile satar man fetur, in ji Danjuma a wata sanarwa da ya fitar.

Reuters