NIjeriya dai ta dade tana kokarin dakile ayyukan matatun danyen mai ba bisa ka'ida ba. Hoto / Reuters 

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta lalata haramtattun matatun mai a yankin kudancin kasar, a wani harin da ta kai ta sama a jihar Ribas da ke kudancin kasar.

Rundunar ta ce ta kai hare-haren ne a ranakun Litinin da Talata inda ta kara da cewa ta lalata wasu kwale-kwale da wuraren ajiyar kayayyakin aiki na barayin danyen mai.

Gudanar da matatun mai ba bisa ka'ida ba ya zama ruwan dare a Nijeriya - daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin mai a nahiyar Afirka.

"Za a ci gaba da kai wannan samame har sai an samu galaba wajen dakatar ko rage ayyukan bata-gari," a cewar sanarwar da mai managa da yawun rundunar sojojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya fitar ranar Laraba.

Ana yawan gudanar da ayyukan daruruwan haramtattun matatun mai a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur a Nijeriya.

Kasar dai tana ci gaba da yaki don dakile masu haka haramtattun matatun mai a daidai lokacin da ake zargin cewa akwai hannun manyan 'yan siyasa da jami'an tsaro a wadannan munanan ayyuka.

An lalata kwale-kwale da tafkunan ruwa da tankunan ajiyar mai a yayin samamen sojin.

Nijeriya na da kusan ganga biliyan 37 na arzikin danyen mai, a cewar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta Opec.

TRT Afrika