Dakarun rundunar hadin gwiwa ta HADARIN DAJI da ke aikinta a Arewa maso Yammacin Nijeriya ta ce ta samu nasarar ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su a Jihar Sokoto.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a ranar Laraba, ta ce an ceto mutanen ne a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba bayan kai samame ƙauyen Alya Fulani da dajin Buani da ke ƙaramar hukumar Tangaza.
“Jajirtattun dakarun rundunar Hadarin Kaji ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut na ci gaba da kai zafafan hare-hare kan 'yan ta'adda a yankunan da suke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Yamma,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa “an gano maɓoyar dukkan ƴan ta’addan tare da lalata su, lamarin da ya sa suka tsere suka kuma bar mutanen da suke garkuwa da su a wajen, kafin isar zaƙaƙuran dakarun.”
Daga nan sai dakarun suka wuce ƙauyen Goboro inda suka ceto wata mace ɗaya da aka yi garkuwa da ita, bayan guduwar ƴan bindigar da suka tsare ta sakamakon fin ƙarfinsu da sojojin suka yi.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da ƴan bindiga ke yawan kai hare-hare ƙauyukansu da kuma yin garkuwa da mutane.
Sai dai a baya-bayan nan hukumomin tsaron Nijeriya suna cewa suna samun galaba sosai a kan ƴan bindigar.