Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kai samame wata maɓoyar ‘yan ƙungiyar IPOB mai fafutikar kafa ƙasar Biafra a dajin Igboro da ke Jihar Abia a ranar Asabar inda ta kashe mambobin ƙungiyar shida.
A sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce dakarunta na Operation UDO KA ne suka kai samamen domin kama waɗanda suke da hannu a kisan sojoji biyar a garin Aba a makon da ya gabata.
“Domin kama waɗanda suka kai hari kan dakarunmu (uku cikin waɗanda aka kashe ‘yan asalin kudu maso gabas ne) a Aba a makon da ya gabata da kuma ƙwato makamai daga masu fafutikar kafa ƙasar Biafra da ƙawayenta na Eastern Security Network terrorist group, dakarun Operation UDO KA sun samu nasarar kai wani samame a sansanin IPOB/ESN da ke dajin Igboro a Ƙaramar Hukumar Arochukwu da ke Abia,” in ji sanarwar.
A yayin samamen wanda aka kai bayan samun bayanan sirri, dakarun sun haɗu da ababen fashewa a kan hanya inda soja ɗaya ya jikkata.
Sojojin sun ce sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan wanda hakan ya kai ga sun kashe shida daga cikinsu, inda sauran suka gudu cikin daji ɗauke da raunin harbin bindiga a jikinsu.
Sojojin sun ce sun ƙwato bindigogi uku na gargajiya da makamakin RPG na gargajiya da makaman atilare biyu su ma na gargajiya da mazauninsu.
Sauran makaman da suka samu sun haɗa da bindiga irin ta gargajiya da tutocin Biafra da Toyota Tundra da motoci ƙirar Hilux waɗanda aka ƙona.