Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce sojojin ƙasar sun samu nasarar kama wani riƙaƙƙen ɗan ta’adda mai suna Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Habu Dogo.
A wata sanarwa da daraktan ayyuka na hedkwatar tsaron Nijeriya Edward Buba ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa kamun da aka yi wa Habu Dogo babban ci gaba ne ta ɓangaren yaƙi da ta’addanci da gwamnatin ƙasar ke yi.
Kafin kama shi, Habu Dogo na daga cikin jerin ‘yan ta’addan da ƙasashen Nijeriya da Nijar ke nema sakamakon irin ta’addancin da yake aikatawa.
Sojojin na Nijeriya sun tabbatar da cewa an kama Habu a ƙauyen Rumji da ke Ƙaramar Hukumar Illela ta Jihar Sokoto.
Sojojin na Nijeriya a ‘yan kwanakin nan suna yawan sanar da nasarorin da suke samu a kan ‘yan ta’adda musamman a arewa maso yammaci da maso gabashin Nijeriya.
Ko a kwanakin baya sai da sojojin suka tabbatar da kashe Halilu Sububu wanda shi ne mai gidan su Bello Turji da wasu gawurtattun ‘yan ta’adda a arewacin Nijeriya.