Sojojin na Nijar sun kwace iko da gwamnatin kasar tun a ranar 26 ga watan Yuli. Hoto/Others

Sojojin da ke mulki a Nijar sun yi wa jakadan kasar da ke Ivory Coast kiranye a ranar Litinin domin tattaunawa da shi, kamar yadda mai magana da yawunsu ya bayyana.

Sun dauki matakin ne bayan shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya bayyana niyyarsa a fili ta tura dakarunsa Nijar domin tunkarar sojojin kasar.

Kakakin sojin na Nijar Amadou Abdramane a yayin jawabin da ya yi ta talabijin din kasar ya bayyana cewa burin Shugaba Ouattara a halin yanzu shi ne ya ga an aiwatar da wannan “rashin hankalin da zalunci a kan Nijar.”

A karshen taron da ECOWAS ta yi a Nijeriya a makon jiya, shugabannin kungiyar sun ce diflomasiyya ce zabi mafi kyau ta magance rikicin siyasar Nijar.

Sai dai sun jaddada cewa za su iya amfani da karfin soji idan lamarin ya kai makura, tare da bayar da umarni ga dakarun sojinsu su kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da Nijar kan tsarin dimokuradiyya.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abidjan na Ivory Coast bayan taron ECOWAS, Shugaba Ouattara ya bayyana cewa ya bayar da umarni ga shugaban sojojin kasarsa su soma “tattara dakarunsu domin shiga aikin ECOWAS”, kuma a shirye Ivory Coast take ta bayar da sojoji 850 zuwa 1,100 don yin wannan aiki.

A ranar Litinin, ECOWAS ta yi watsi da shirin shugabancin Nijar na tuhumar Shugaba Bazoum wanda sojojin kasar suka hambarar a ranar 26 ga watan Yuli.

ECOWAS ta bayyana matakin a matsayin tsokanar fada.

A ranar Lahadi, mai magana da yawun sojin Nijar ya bayyana cewa “za a tuhumi Bazoum da cin amanar kasa da yin kafar-ungulu kan tsaron cikin gida da wajen Nijar."

Rahotanni sun ce Bazoum da dansa da matarsa na tsare a fadarsa da ke Yamai babban birnin kasar tun bayan da sojojin suka hambarar da shi.

Janar Abdourahamane Tchiani, tsohon kwamandan tsaron fadar shugaban kasar Nijar, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin sojin Nijar.

AA