Wata kotun soji a Jamhuriyar Nijar ta saki Salem, wato dan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Kotun ta CNSP ta bayar da sanarwa Salem Bazoum ne a wata takarda da ta fitar ranar Litinin da maraice.
Sanarwar ta ce an mika shi ga Ministan Harkokin Waje na Togo Robert Dussey, kuma tuni suka fita daga kasar zuwa birnin Lome.
An yi wa Salem, mai shekara 23, daurin-talala tare da mahaifansa a gidan shugaban kasa da ke Yamai tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Juyin mulkin, wanda shi ne na takwas da sojoji suka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga 2020, ya jawo wa kasar bakin-jini, har ya kai ga kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta sanya mata takunkumi yayin da kuma kasashen duniya suke ta kiraye-kiraye a Bazoum tare da mika mulki ga gwamnatin dimokuradiyya.
Kotun ba ta yi bayani game da makomar Bazoum da mai dakinsa ba.
Hukuncin kotun ECOWAS
A watan jiya, kotun ECOWAS ta ce daurin-talalar da aka yi wa Bazoum da iyalansa ya keta doka inda ta bukaci a sake shi sannan a mayar da shi kan mulki.
Kotun, wadda ba a daukaka kara kan hukuncin da ta yanke, ta bai wa sojojin Nijar wa'adin wata daya su bayyana mata yadda za su aiwatar da umarninta, a cewar lauyoyi.
Labarai masu alaka:
Sojojin suna tuhumar Bazoum da dansa Salem bayan juyin mulkin da suka yi ranar 26 ga watan Yuli. An zargi Salem da hada baki wajen yunkurin yin tarnaki ga hukumomi da tsaron Nijar.
An katse ruwa da lantarki a gidan da Bazoum da iyalansa suke ciki tun da sojoji suka yi masa juyin mulki, a cewar jami'an jam'iyyarsa da kuma 'yan'uwansa.
A baya, lauyansa ya ce an hana shi zuwa kotu domin yin karar sojojin da suka yi juyin mulki.