A wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin, Aljeriya ta ce ta karɓi saƙon amincewar Nijar kan shirin Shugaba Abdelmadjid Tebboune na shiga tsakani / Photo: AA

Jamhuriyar Nijar ta amince da tayin da Aljeriya ta yi mata na neman shiga tsakani a rikicin siyasarta, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta faɗa, mako biyar baya da Aljeriyan ta tsara wa Nijar ɗin wani shirin miƙa mulki ga farar hula a tsawon wata shida.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin, Ma'aikatar ta ce Aljeriya ta karɓi saƙon amincewar Nijar kan shirin Shugaba Abdelmadjid Tebboune na shiga tsakani.

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bai wa Ministan Harkokin Wajen kasar Ahmed Attaf umarnin "ziyartar Niamey ba tare da ɓata lokaci ba da nufin fara tattaunawar... tare da dukkan masu ruwa da tsaki," a cewar sanarwar.

Sai dai har yanzu ba a ji ta bakin sojojin juyin mulkin na Nijar ba kan sanarwar.

Komawa kan tafarkin tsarin mulki

A ƙarshen watan Agusta, Attaf ya ce Aljeriya ta yi magana a lokuta da dama da shugabannin mulkin sojin Nijar tare da samar da wani shiri na mayar da ƙasar kan turbar tsarin mulki.

Aljeriya ta ce za ta samar da tsarin da za a yi wa kowanne ɓangare da rikicin ya shafa adalci da kuma ɗaukar nauyin wani taro da zai yi duba kan ci gaban yankin Sahel.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a watan da ya gabata ya ce yana neman mayar da doka bisa tsarin mulki tare da magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki a Nijar, ya kuma yi maraba da duk wani goyon baya da zai taimaki tsarin.

Tinubu shi ne shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, wacce take ta ƙoƙarin sasantawa da sojojin juyin mulkin Nijar.

ECOWAS ta ce tuni ta girke dakaru idan har ƙoƙarin diflomasiyya na mayar da doka bai yi nasara ba.

TRT World