Ana yawan zargin sojojin hayar Rasha na Wagner da take hakkin bil adama. Hoto/Reuters

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bukaci tallafin sojoji daga rundunar sojojin haya ta Wagner a daidai lokacin da wa’adin da kungiyar ECOWAS ta bayar na mika mulki ga farar hula ke kawo karshe.

Neman agajin na zuwa ne a lokacin da daya daga cikin jagororin juyin mulkin, Janar Salifou Mody ya je Mali mai makwaftaka, inda ya hadu da wani daga rundunar ta Wagner, Wassim Nasr, kamar yadda wani dan jarida kuma babban mai bincike a Cibiyar Soufan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Ya bayyana cewa wasu majiyoyi uku daga Mali da kuma wani jami’in diflomasiyya na Faransa ya tabbatar da tattaunawar wadda gidan talabijin na France24 ya soma bayar da labari a kai.

“Suna bukatar (Wagner) saboda za su zama wani tabbaci a gare su na rike mulki,” in ji shi, inda suka kara da cewa rundunar na duba bukatar ta su.

Wa’adin ranar Lahadi

Wani jami’in soji na daya daga cikin kasashen Yamma wanda bai so a bayyana sunansa domin ba a amince ya yi magana ba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa su ma sun ji labarin cewa sojojin na Nijar na neman taimako daga Wagner da ke Mali.

Zuwa ranar Lahadi ne wa’adin sojin Nijar din da kungiyar ECOWAS ta bayar ke karewa domin saki da kuma mayar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mukaminsa.

Shugabannin tsaro na kasashen ECOWAS sun cimma matsaya kan cewa amfani da karfin soji a ranar Juma’a inda suka bukaci sojojinsu da su zama cikin shiri bayan da aka tura masu shiga tsakani Nijar a ranar Alhamis inda aka ki barin su gana da shugaban kasar na mulkin soji Janar Abdourahmane Tchiani.

‘Sabuwar Libiya’

Bayan ziyarar da ya kai Mali, Mody ya yi gargadi kan amfani da karfin soji inda ya sha alwashin cewa Nijar za ta yi duk mai yiwuwa domin kada ta zama “sabuwar Libiya” kamar yadda kafar watsa labarai ta Nijar ta ruwaito a ranar Juma’a.

Ana kallon Nijar a matsayin aminiya ta karshe da kasashen Yamma suka dogara da ita wurin dakile ta’addanci a yankin da aka yi ta yin juyin mulki a ‘yan shekarun nan.

Sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi watsi da tsohuwar kasar da ta yi musu mulkin mallaka wato Faransa inda suka juya akalarsu zuwa Rasha.

Wagner na ayyuka a wasu kasashen Afirka da suka hada da Mali inda masu kare hakkin bil adama suka zarge dakarun da take hakkin bil adama.

Daga tutocin Rasha

Wani ba zai iya cewa akwai tasirin Rasha kai tsaye kan juyin mulkin Nijar ba, sai dai a bayyana take kan cewa akwai wata dama da Rasha ke da ita, inda take kokarin goyon bayan rashin zaman lafiya a duk inda yake,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa Anne-Claire Legendre a tattaunawarta da BFM a ranar Juma’a.

Tsawon kwanaki bayan da sojojin Nijar suka kwace mulki, mazauna kasar sun ta daga tutar Rasha a kan hanya.

Faransa na da sojoji 1,500 a Nijar, duk da cewa sojojin na Nijar sun ce sun yanke yarjejeniyar tsaro da Paris haka kuma Amurka na da sojoji 1,100 a can.

AP