Shugaban mulkin soji na Mali Assimi Goita yayin sakko wa daga jirgin saman shugaban kasa. Photo / AFP

Tsofaffin ministocin Mali da dama ne suka gurfana a gaban kotu a ranar Talata bisa zargin su da karkatar da miliyoyin daloli a lokacin sayen jirgin Shugaban Ƙasa a 2014 da ma wasu kayan ayyukan soji.

Batun ya yi shuhura a Mali inda shugabannin sojin da ke mulki a yanzu bayan juyin mulkin 2020 suka ce manufarsu ta kifar da gwamnati ita ce kawo ƙarshen cin hanci da rashawa da suka mamaye gwamnatin Boubacar Keita, da kuma gazawar su ta yaƙar 'yan ta'adda da 'yan tawaye.

An sayo jirgin saman Shugaban Ƙasar kan kudi dala miliyan 40 da ma wasu kayayyakin ayyukan soji ba tare da bin ƙa'idoji ba.

Lamarin ya sanya Asusun Bayar da Lamuni na Duniya riƙe kuɗaɗen Mali na tsawon watanni shida.

Tsohon Firaminista

A 2021 an kama tsohon Firaminista Soumeylou Boubeye Maiga, wanda shi ne Ministan Tsaro a lokacin da aka sayi kayan, da tsohon ministan kudi Bouare Fily Sissoko.

An zarge su da almundahana da cin amana da nuna son kai.

Maiga, wanda ya dage kan bai aikata komai ba, ya rasu a kurkuku a watan Maris ɗin bara. Magoya bayansa sun zargi gwamnatin sojin da barin sa ya mutu a kurkuku.

Sauran wadanda ake zargi a almundahanar sun hada da Mahamadou Camara, tsohon shugaban ma'aikatar fadar Shugaban Ƙasar da aka hambarar.

TRT Afrika