Diyar tsohon Shugaban Angola ta karkatar da $57m na gwamnati cikin asusunta

Diyar tsohon Shugaban Angola ta karkatar da $57m na gwamnati cikin asusunta

Wata kotu a Netherlands ta samu Isabel dos Santos, diyar tsohon Shugaban Angola da laifin cin hanci da rashawa.
Ana zaton Isabel dos Santos tana boye ne a Dubai.  Hoto: Reuters      

Isabel dos Santos, diyar tsohon Shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos, ta karkatar da kudi zuwa asusan ajiyarta na banki tsakanin shekarar 2006 zuwa 2017, kamar yadda wata kotu a kasar Netherlands ta ce.

Isabel, mai shekara 48, ta yi aiki da manyan manajoji a kamfanin mai mallakin kasar Angola, Sonangol wajen karkatar da dala miliyan 57, kamar yadda kotun daukaka kara a birnin Amsterdam ta bayyana a ranar Talata.

Hujjojin sun nuna cewa an karkatar da kudin ne zuwa asusan ajiyar Isabel ta hanyar wasu kamfanonin Netherlands masu zaman kansu.

An aikata wadannan laifuka ne lokacin da mahaifin 'yar kasuwar yake Shugaban kasa a Angola.

Kotun daukaka karar ta dora alhaki a kan daraktocin kamfanin mai na Sonangol ta hanyar yin takardun jabu wadanda taimaka wajen aikata cin hancin.

Har ila yau an zargi Isabel da amfani da wani kamfanin bogi wajen sayan hannun jari a kamfanin Sonangol a madadin mijinta, Sindika Dokolo, wanda dan Kongo ne kuma ya rasu ne a watan Oktoban 2020.

Wata kotu a Netherlands a shekarar 2021 ta ce Isabel ta sayi hannun jarin ne ta haramtacciyar hanya. Kamar yadda kotun ta bayyana "an saba wa ka'ida wajen sayan hannun jarin."

Yaki da cin hanci da rashawa

Mahaifin Isabel – wanda ya rasu – ya sauka daga mulki ne a shekarar 2017, wanda hakan ya bai wa wanda ya gaje shi Joao Lourenco damar darewa karagar mulki.

Yayin da hau mulki, Shugaba Lourenco ya kori Isabel daga mukaminta na shugabar kamfanin Sonangol a wani mataki na yaki da cin hanci da rashawa.

Wani bincike da wata kotu ta yi a Netherlands daga bisani ya tabbatar da cewa an sanya hannu a wasu takardun jabun don ta samu damar kabar dala miliyan 57 daga Sonangol da sunan riba.

Kotun ta ce "duka mutanen da suka sanya hannu a takardar sun kwana da sanin cewa an yi amfani da tsohon kwanan wata ne."

Mario Leite de Silva, wani na kusa da Isabel kuma jami'in kudi ne a Sonangol, shi ma an same shi da laifi na hadin baki wajen cin hanci da rashawa.

Maarten Drop, lauyan kamfanin Sonangol, ya ce ya ji dadin hukuncin kotun, inda ya bayyana shi da "abin da zai kara karfafa yaki da cin hanci da rashawa a Angola," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Angola (LUSA) ya bayyana.

Gwamnatin Angola tana kokarin kwato kadadori da kudinsu ya kai biliyan daya na Isabel.

Hukumar 'yan sandan kasa da kasa ta fitar da sanarwar wucin gadin kama ta duk da cewa ta musanta cewa ta amfana daga matsayin da mahaifinta ya rike. Ina zaton Isabel tana boye a Dubai.

TRT Afrika