Tawagar sojojin ta ayyana kawo karshen mulkin Ondimba a sanarwar da ta yi a gidan talabijin.

Mun gode da kasancewa da mu a wannan shafi da ya kawo muku labaran abubuwan da suka faru a Gabin a ranar Laraba - wanda ya mayar da hankali kan sanarwar da sojoji suka yi cewa sun hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba, jim kadan bayan sanar da nasarar tazarce da ya samu a zaben da aka yi ranar Asabar.

Ga dai jerin abubuwan da suka faru a takaice:

  • An yi wa Shugaba Bongo daurin talala
  • Dan shugaban kasar na cikin muatnen da aka kama ake tsare da su
  • Shugaban kasar ya nemi taimakon abokansa
  • Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Alla wadai da abin da ta kira yunkurin juyin mulki
  • Faransa da China da Russia da Amurka sun nuna damuwa kan halin da ake ciki a Gabon.

17:00 GMT - Wadanne burika Faransa take da su na kasuwanci a Gabon?

Kamfanonin Faransa suna da burika na tattalin arziki daban-daban a Gabon.

Akwai kamfanoni 80 na Faransa da aka yi wa rajista a Gabon, baya ga kananan harkokin kasuwanci da 'yan kasuwa da shagunan sayar da abinci da lauyoyi da sauran kamfanoni na harkokin kudi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

A shekarar 2022 Gabon ta zama babban wajen fitar da kayayyaki na Faransa daga cikin kasashe shida mambobin Kungiyar Raya Tattakin Arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka CEMAC.

Kamfanonin Faransa sun sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai dala miliyan 585 a Gabon, a cewar alkaluman ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Kamfanin hakar ma'adanai na Eramet, daya daga cikin manyan kamfanonin Faransa a Gabon, ya dauki mutum 8,000 aiki a kasar mai arzikin fetur da sauran ma'adanai, da kuma ma'adanin manganese ore - wanda ake amfani da shi wajen hada batiri.

Gabon ita ce kasa ta biyu a duniya da ta fi samar da ma'adanin manganese baya ga Afirka ta Kudu, South Africa, kuma kamfanin Comilog yana kwasar kashi 90 cikin 100 na ma'adanin manganese din Gabon, inda wani kamfanin China CICMHZ kuma ke amfani da sauran.

Sannan kuma kamfanin Eramet ne yake kula da harkar sufurin layin dogo na Gabon.

Kazalika tun shekarar 1928 kamfanin fetur na TotalEnergies yake Gabon, wanda shi ne kamfani na hudu mafi girma da ke samar da fetur a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka kuma mamba a kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta OPEC.

Kamfanin Maurel and Prom, mai aikin hako ma'adanin hydrocarbon a ranar Laraba ya ce halin da ake ciki a Gabon bai shafi wuraren da yake aiki ba kuma kasuwanci na ci gaba da tafiya yadda ya kamata.

Kamfanin man fetur na Perenco wanda shi ma yake da tasiri a Gabon, bai ce komai ba a lokacin da AFP ta tuntube shi.

15:45 GMT - Dan shugaban kasa na cikin manyan mutanen da aka kama a Gabon

Manyan jami'an sojin da suka kwace mulki a Gabon a ranar Laraba sun kama tare da tsare manyan mutane da dama, a cewar sojojin juyin mulkin.

Noureddine Bongo Valentin, dan shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba da shugaban Majalisar Dokokin Kasar Richard Auguste Onouviet suna tsare, kamar yadda sojojin juyin mulkin wadanda aka fi sani da Kwamitin Mika Mulki da Farfado da Hukumomi (CTRI) suka ce.

Tawagar sojojin ta ayyana kawo karshen mulkin Ondimba a sanarwar da ta yi a gidan talabijin bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na zaben da aka yi a ranar Asabar.

Shugaba Bongo ya yi nasara da fiye da kashi 64% na yawan kuri'un.

"An yi kwange" a sakin duka sakamakon zaben, kuma an soke zaben, a cewar mai magana da yawun sojojin da suka yi juyin mulkin.

Wadanda suka kitsa juyin mulkin sun sanar da kama manyan mutane da yawa kan "laifin cin amanar kasa da almubazzaranci da kudin al'umma da cin hanci da safarar miyagun kwayoyi da sauran manyan laifuka."

Kwamitin CTRI ya ce ba zai lamunci ci gaba da mulkin "gwamnatin da ba ta san ciwon kanta ba wacce take jawo lalacewar zamantakewa da neman saka kasar cikin rikici."

Sojoji na fareti bayan hambarar da shugaban kasar Gabon.

15:30 GMT - Turkiyya 'tana sa ido sosai a nutse' kan halin da ake ciki a Gabon situation

Turkiyya tana sa ido kan halin da ake ciki a Gabon cikin "sosai kuma cikin nutsuwa", kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fada a ranar Laraba.

"Muna fatan zaman lafiya mai dorewa zai koma a kasar kamar yadda take a baya," a cewar sanarwar ma'aikatar.

15:00 GMT - An yi wa shugaban Gabon Ali Bongo 'ritaya' - sojoji

Shugaban tawagar sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa Gabon ya ce an yi wa Shugaba Ali Bongo "ritaya," kamar yadda ya shaida wa jaridar Le Monde a ranar Laraba bayan da sojojin da suka yi tawaye suka hambarar da mulkinsa.

"An yi masa ritaya. Yana da dukkan 'yancinsa. Shi dan kasar Gabon ne kamar sauran mutane," a cewar Brice Oligui Nguema yayin da yake musanta cewa shi ne jagoran sojojin da suka hambarar da mulkin.

An ga Shugaban Rundunar Sojin da ke Gadin Fadar Shugaban Kasar a wani bidiyo yana gabatar da jawabi a gidan talabijin na kasar a ranar Laraba, inda daruruwan sojoji ke sowa suna cewa "Oligui president."

Da aka tambaye shi ko me ya sa suka hambarar da Bongo, sai ya ce wa jaridar: "Ba a yin abubuwa yadda suka kamata a Gabon, baya ga haka kuma shugaban kasar ba shi da lafiya. Kowa ya damu da hakan, amma babu wanda yake yin wani abu a game da hakan.

"Ba shi da damar da zai sake tazarce karo na uku. An take dokar kundin tsarin mulki. Tsarin zaben da aka bi bai dace ba. Don haka sojoji suka yanke hukuncin daukar matakin da ya dace."

Tun shekarar 2018 Bongo ke fama da matsalar shanyewar barin jiki, lamarin da ya sa dole ya daina fita bainar jama'a, saboda ba ya iya motsi da magana sosai.

A ranar Laraba da safe ne hukumar zabe ta Gabon ta sanar da nasarar Bongo a karo na uku, inda ya yi nasara da kashi 64.27 na yawan kuri'un bayan zaben da aka gudanar mai cike da matsaloli.

14:00 GMT - Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi ‘Allah-wadai da yunkurin juyin mulki’ a Gabon

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan abin da ta kira da juyin mulki a Gabon, wanda sojoji suka yi wa Shugaba Ali Bongo Ondimba daurin-talala.

Ta bayyana cewa kwace iko da sojoji suka yi ya saba wa kundin tsarin mulki, kamar yadda sanarwar da Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayar ta bakin Moussa Faki Mahamat.

Ya yi kira ga sojoji da su tabbatar da lafiyar shugaban kasar da iyalansa da sauran mutanen da ke cikin gwamnati.

13:30 GMT - Shugaban Nijeriya ya ce yana aiki da shugabannin Afirka wajen samo mafita

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ya ce yana aiki kut-da-kut da shugabannin Afirkakan matakin da ya kamata su dauka kan yunkurin juyin mulki a Gabon, a cewar mai magana da yawun Tinubun.

Tinubu yana sa ido sosai kan abin da ke faruwa a Gabon da masu yi wa dimokuradiyya zagon kasa da ke yaduwa a nahiyar cikin "tsananin damuwa," in ji mai magana da yawun shugaban Nijeriyar.

13:00 GMT - Kungiyar Commonwealth ta ce juyin mulkin Gabon abin damuwa ne matuka

Kungiyar Kasashen Rainon Ingila ta Commonwealth ta bayyana damuwarta kan juyin mulkin da aka yi a Gabon, wacce ta shiga kungiyar a bara, sannan ta ce tana bin diddigin lamarin sosai.

Sakatare janar Patricia Scotland a ranar Talata ta ce lamarin "abin damuwa ne matuka."

Ta kara da cewa: "Kungiyar Commonwealth ta fayyacewa dukkan mambobinta cewa dole dukkansu su bi tsarin doka da oda da girmama dokokin dimokuradiyya a kowane lokaci."

12:00 GMT Bongo ya nemi agajin abokansa a fadin duniya

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya bayyana a wani bidiyo inda ya yi kira ga "abokaina" su yi "magana" bayan sojoji sun kifar da gwamnatinsa.

"Ina tura sako ga dukkan abokanmu da ke fadin duniya su yi magana (…) mutane a nan sun tsare ni da iyalaina," in ji shi, fuskarsa cike da damuwa, a bidiyon da aka watsa a shafukan intanet. Ba a tantance lokacin da aka dauki bidiyon ba.

11:30 GMT - Intanet ya dawo a Gabon - Netblocks

An mayar da internet a Gabon bayan da ya aka shafe kwana uku ba ya aiki, bayan da sojojin kasar suka sanar da kwace mulki.

Sai dai intanet din ba gaba daya ne ya koma aiki ba, a cewar wani kamfanin ula da intanet din, Netblocks.

Gwamnatin Gabon ce ta tursasa rufe intent din gaba daya a kasar a lokacin da ake dab da kammala zaben kasar a ranar Asabar, da nufin hana yada labaran karya da kuma rikicin da ka iya barkewa a kasar.

11:50 GMT - China ta yi kira a tabbatar da tsaron lafiyar Bongo

China ta yi kira ga "dukkan bangarorin" da ke Gabon su tabbatar da tsaron lafiyar Shugaba Ali Bongo Ondimba bayan sojoji sun ce sun "kawo karshen wannan gwamnatin".

"China tana bibiyar abin da ke faruwa a Gabon sau da kafa," a cewar kakakin ma'aikatar wajen kasar Wang Wenbin a sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

"Muna kira ga dukkan bangarorin na Gabon su kare muradun kasar da na 'ya'yanta, su kawo karshen matasalar cikin lumana sannan su dawo da komai kan hanya nan ba da jimawa ba," a cewarsa. inda ya yi kira da a "tabbatar da tsaron lafiya Shugaba Bongo".

11:00 GMT Faransa ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon

Gwamnatin Faransa ta yi tur da juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon sannan ta yi kira a gare su da su mutunta sakamakon zaben shugaban kasar, kamar yadda mai magana da yawun gwamatin kasar ya bayyana.

Faransa ta yi kira ga sojoji su mutunta sakamakon zaben shugaban kasar Gabon./Hoto:Reuters

10:30 GMT An yi wa Shugaba Ali Bongo daurin-talala

Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun yi wa hambararren shugaban kasar Ali Bongo Ondimba daurin-talala sannan suka tsare dansa bisa zargin “cin amanar kasa”.

Sun bayyana haka ne sa’o’i kadan bayan sun sanar da kifar da gwamnatinsa.

"An yi wa Shugaba Ali Bongo daurin-talala inda yake tare da iyalansa da likitocinsa," a cewar sanarwar da aka karanta a gidan talabijin na kasar ranar Laraba.

TRT Afrika da abokan hulda