Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin sun tsare shi a wani wuri sannan suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya. / Hoto: AFP

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ki amincewa su saki iyalansa.

Ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a yayin da ya tattauna ta wayar tarho da tsohon shugaban Nijar Mohamed Issoufou kan halin da Bazoum ke ciki.

Ana ta nuna fargaba game da halin da Bazoum da matarsa da kuma dansa mai shekara 20 suke ciki tun bayan da sojoji suka yi masa juyin mulki ranar 26 ga watan Yuli.

"Sakatare ya nuna matukar mamaki kan yadda sojojin da suka kwace mulki a Nijar suka ki sakin iyalan Bazoum domin su nuna jinkai," in ji wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Wajen Amurka Matthew Miller ya fitar.

Blinken ya bayyana "matukar damuwa" game da yadda sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum suke ci gaba da tsare shi da iyalansa cikin "mawuyacin hali".

Mohamed Issoufou shi ne shugaban kasar da ya mika mulki ga Bazoum a watan Afrilun 2021 bayan ya lashe zaben shugaban kasar. Sannan shi ne babban 'uban gidansa' a siyasa.

Da ma dai Amurka ta ce za ta dora alhakin duk wani abu da ya samu zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa da 'yan majalisar gwamnatinsa da ke tsare, kan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

Ta fadi hakan ne bayan Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin sun tsare shi a wani wuri sannan suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.

Amurka ta kuma goyi bayan ECOWAS saboda matakinta na sanya dakarunta cikin damarar yaki da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Karin zanga-zanga

A ranar Juma'a ne daruruwan 'yan kasar ta Jamhuriyar Nijar suka yi karin zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Masu gangamin sun rika jinjina wa jagoran sojojin da suka yi juyin mulki Abdourahamane Tchiani./Hoto:Reuters

Masu zanga-zangar, wadanda suka je sansanin sojojin Faransa da ke kasar wasunsu rike da tutocin Rasha, sun rika jinjina wa jagoran sojojin da suka yi juyin mulki Abdourahamane Tchiani.

Sun yi tir da duk wani kutse da suka ce ECOWAS tana kokarin yi musu sannan suka sha alwashin kare kasarsu.

A nata bangare, Rasha ta gargadi ECOWAS game da yiwuwar tura sojojinta kasar Nijar tana mai cewa hakan zai iya haifar da "taho-mu-gama da za a dade ana yi".

TRT Afrika