Shugaba Tinubu ya bukaci kasashen Afirka su hada kai domin cimma manufa iri daya./ Hoto: Tinubu/Facebook

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gargadi manyan kasashen duniya game da ci gaba da sace albarkatun nahiyar Afirka.

Ya yi gargadin ne a jawabin da ya gabatar a wurin taron shugabannin Afirka da aka yi a Nairobi babban birnin Kenya ranar Lahadi.

"Wannan duniyar da muke ciki ba ta da adalci kuma tana da rashin tabbas. Abubuwan da suka faru a tarihi da kuma abubuwan wahala da ke faruwa yanzu a duniya na zama kalubale wajen samun nasararmu,’’ in ji shugaban na Nijeriya.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin da manyan kasashen duniya ke ci gaba da gogayya da juna domin yin tasiri a Afirka abin da masana ke gani wani bangare ne na tatsar albarkatun kasar nahiyar.

Shugaba Tinubu ya yi tir da wannan "sabon tsari na neman gindin zama a Afirka," inda ya yi kira ga kasashen nahiyar su hada kai domin cimma manufa iri daya.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Dele Alake ya fitar ta ambato shugaban Nijeriya na cewa "Ba za a maimaita abin da ya faru a baya na barnatar da albarkatun nahiyar ba."

Makomar Afirka

Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar ganin Afirka ta shawo kan matsalolinta sannan ta yi "aiki domin samun makoma ta gari, ta hanyar mayar da hankali kan ci-gabanta da mulki na gari da samar da damarmakin kasuwanci mara shinge na Afirka wato African Continental Free Trade Area (AfCFTA).’’

‘’Kasashenmu za su tsinci kansu a cikin mawuyacin hali idan muka ci gaba da zama 'yan kallo game da makomarmu," in ji shi. "Wasu masana na ganin tuni aka soma sabuwar gogayyar kwashe albarkatun kasar Afirka kuma hakan ya yi kama da abin da ya faru a baya," a cewar Shugaba Tinubu.

''Amma muna son sanar da sabbin masu kokarin kwashe albarkatunmu a nan wurin kuma yanzu, cewa ko da yake Afirka ta tsufa amma fatanmu sabo ne. Kuma muna da karfin hali. Dole mu hana abin da ya faru a baya,''a cewarsa.

TRT Afrika