Nijar

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bukaci Kotun Afirka ta Yamma ta ECOWAS da ta ba da umarnin dage takunkuman da maƙwabtanta suka ƙaƙaba wa kasar sakamakon juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, inda aka hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban kasar.

"Babu wani bangare na al’ummar Nijar da wadannan takunkuman ba su shafa ba” wadanda suka janyo wahalhalu na tattalin arziki a daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, a cewar Youkaila Yaye, daya daga cikin lauyoyin gwamnatin mulkin sojan, yayin da yake yi wa kotun jawabi a zaman da aka yi a ranar Talata a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Bayan da manyan sojoji suka hamɓarar da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, kasar ta fuskanci takunkuman tattalin arziki daga kungiyar ECOWAS da kuma wasu kasashen da suka hada da Amurka da suke bayar da agajin kiwon lafiya da tsaro da kayayyakin more rayuwa.

Makwabtan kasashe sun rufe iyakokinsu da Nijar kuma an katse sama da kashi 70 na wutar lantarkinta, wacce Nijeriya ke bayarwa, bayan dakatar da hada-hadar kudade da kasashen Yammacin Afirka.

An rufe kadarorin Nijar a bankunan kasashen waje tare da hana daruruwan miliyoyin daloli na agaji.

Takunkuman su ne mafi tsauri da kungiyar kasashen yankin ta ƙaƙaba wa ƙasar, a yunƙurin da take yi na daƙile juyin mulki a yankin Sahel na Afirka mai fama da rikici.

Sai dai ba su yi wani tasiri ko kadan ba wajen rage burin gwamnatin mulkin sojan, wadda ta ci gaba da nuna ƙarfin ikonta yayin da miliyoyin mutane a Nijar ke fuskantar ƙunci.

A yayin zaman kotun, lauyoyin gwamnatin sun bayyana yadda takunkuman ke cutar da Nijar: Yara ba sa iya komawa makaranta saboda ƙarancin kayayyaki. Kayayyaki na ƙarewa a shagunan sayar da magunguna. Harkokin kasuwancin sun tsaya cak saboda tsadar kayayyaki.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun yanke huldar soji da Benin

Yaye ya zargi ECOWAS da ladabtar da ‘yan Nijar kan juyin mulkin ta hanya mai tsauri fiye da yadda ta yi ga wasu kasashen da aka yi juyin mulki, “musamman dangane da hada-hadar kudi.

Gwamnatin mulkin sojin ta bukaci kotun da ta sassauta takunkuman har sai an yanke hukunci. Sai dai ECOWAS ta nuna rashin amincewa da bukatar tasu.

Lauyan ECOWAS, Francois Kanga-Penond, ya ce ba a amince da gwamnatin mulkin soja a karkashin tsarin kungiyar ba kuma ba ta da ikon shigar da irin wannan ƙara a kotu.

Kotun ta dage zaman har zuwa ranar 7 ga watan Disamba.

AP