Daraktan watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya Air Commodore Edwarda Gabkwet ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar.

Rundunar sojin sama da ke aiki a Arewa maso Yamma da Areewa ta Tsakiyar Nijeriya ta yi nasarar kai hare-haren sama wasu maɓoyar ƴan ta’adda da dama tare da kawar da su a ƙaramar hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.

A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya Air Commodore Edwarda Gabkwet ya fitar a ranar Lahadi da marece, ya ce an kai harin ne bayan samun wasu bayanan sirri.

Bayanan sirrin sun gano maɓoyar wani gagrumin mai satar mutane da aka fi sani da Boderi tare da ɗan’uwansa da sauran mambobinsu a ƙauyen Tsauni Doka da ke yankin.

“Rundunar sojin Nijeriya a ƙarƙashin samamen Whirl Punch sun kai hare-haren sama a kan ƴan ta’addan da ke ayyukansu a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar ƙasar, lamarin da ya jawo aka kawar da ƴan ta’adda da dama a ƙauyen Tsauni Doka da ke ƙaramar hukumar Igabi,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa an kai hare-haren ne a ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba “inda aka yi wa ƴan ta’addan rugu-rugu.”

“Sannan an kai wasu hare-haren da aka yi nasara a wasu wuraren da ke da nisan mita 500 daga gabashin inda Boderi yake, inda aka yi amannar maɓoyar ɗan’uwansa Nasiru ne.

“An kashe ƴan ta’adda da yawa tare da lalata baburansu," kamar yadda sanarwar rundunar sojin saman ta faɗa.

Rundunar sojin saman ta ce Boderi da abokan aikinsa ne suka kai mafi yawan hare-hare da sace mutane da aka dinga yi a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna da kuma na Kaduna da zuwa Birnin Gwari da ma sauran wasu yankunan a jihohin Kaduna da Neja.

Wani samamen daban a Birnin Gwari

A wani lamarin mai kama da wancan, dakarun na Nijeriya sun kawar da ƴan bindiga shida a wasu samame da suka kai ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin cikin gida da tsaro ta Jihar Kaduna ta ce dakarun sun fara samamen nasu ne a kan titin Kaduna-Sabon Birni-Dogon Dawa, inda suka kai hari ƙauyukan Maidaro da Ngede Allah, kafin daga bisani su wuce zuwa yankunan Saulawa da Kidandan.

“A wannan samamen ne dakarun suka ci karo da Maidaro a yankin Ngade Allah da Kidandan. A nan dakarun suka yi maza suka fi ƙarfin ƴan bindiga ta hanyar rutsa su daga kowane ɓangare. An kawar da mutum shida.”

Dakarun sun kuma bincike yankin tas inda suka gano makamai da dama da suka hada da bindigogin AK-47 da jigidar harsasai da kakin soji da babura da sauran wasu makaman.

Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana gamsuwarsa kan nasarar da dakarun suka cimma tare da jinjinawa rundunar musamman ta Whirl Punch da shugabanninta.

TRT Afrika da abokan hulda