Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta ɗane karagar mulki bayan mutuwar shugaba John Magafuli a shekarar 2021/Hoto; Wasu      

Shugabar ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a jiya Laraba ta kori Ministar Lafiya Ummy Mwalimu wadda ta daɗe tana riƙe da muƙamin a wani ɓangare na garambawul da ta yi wa majalisar ministocinta.

Ana kallon matakin a matsayin wani yunƙuri na sake fasalin gwamnatin Shugaba Samia gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren gwamnatin ƙasar Moses Kusiluka ya fitar, shugabar ta naɗa Jenista Mhagama a matsayin sabuwar babbar ministar lafiya ta ƙasar.

Mhagama ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramar minista a ofishin Firaminista mai kula da tsare-tsare da ayyukan 'yan majalisa.

Mwalimu, wadda ta jima da sanin ilimin kiwon lafiya, ba ta taɓa yin aiki a wannan fanni ba.

Ƙarfafa shugabanci

Har ilau, a garambawul ɗin da ta yi, Shugaba Samia ta naɗa fitaccen farfesa a fannin shari'a Palamagamba Kabudi a matsayin ministan kundin tsarin mulkin ƙasa da shari'a, muƙamin da Pindi Chana ke riƙe da shi a baya.

Ita kuma Chana an naɗa ta a matsayin ministar albarkatun ƙasa da yawon bude ido, matsayin da ta taɓa riƙewa a baya.

Shugabar ta kuma ƙara wa William Lukuvi muƙamin ƙaramin minsita a ofishin firaminista, wanda aka ɗorawa alhakin kula da tsare-tsare da ayyukan 'yan majalisa.

Kazalika garambawul ɗin ya haɗa da wasu muhimman sauye-sauye a ofishin babban mai shari’a, inda aka naɗa babban ƙwararre a harkar sufurin jiragen sama, Hamza Johari, a matsayin wanda ya maye gurbin Eliezer Feleshi da aka naɗa a matsayin alƙalin kotun ɗaukaka ƙara.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi wa majalisar ministocinta garambawul ƙasa da wata guda.

A watan da ya gabata ta kori wasu manyan ministoci guda biyu.

Matakin dai na nuni da irin koƙarin da Shugaba Samia ke ci gaba da yi na ƙarfafa ayyukan gwamnati da harkokin mulki a Tanzania, yayin da ƙasar ke ci gaba da lalubo hanyoyin kawar da ƙalubalen ci gabanta.

AA