Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sallami ministan kuɗi na ƙasar ba tare da bayar da wani dalili ba, duk da cewa sallamar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da hauhawar farashi da kuma karyewar darajar kuɗin ƙasar.
An sanar da korar Bak Barnaba Chol daga aiki a ranar Juma'a inda aka karanto kudirin shugaban ƙasar na korar a talabijin.
A daidai lokacin da matsalolin tattalin arziƙi ke ƙara ƙaruwa a ƙasar, wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati sun shafe watanni shida ba tare da albashi ba.
A ƴan watannin da suka gabata, kuɗin ƙasar wato fam, ta rasa darajarta matuƙa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wanda hakan ya jawo hauhawar farashin kayayyaki.
Tattalin arziki mai rauni
Sudan ta Kudu na ci gaba da gwagwarmaya sakamakon cewa ƙsar wadda ta sha fama da yaƙin basasa tsakanin 2013 zuwa 2018 na ƙoƙarin farfaɗowa, haka kuma ta dogara ne daga sayar da ɗanyen man fetur domin samun kuɗaɗen shiga.
A watan Yulin 2020, wani jami'in Babban Bankin Sudan ta Kudu ya sanar da cewa kuɗaɗen waje na ƙasar sun ƙare wanda hakan zai ci gaba da sa kuɗin ƙasar darajarsu na karyewa.
Chol mai shekara 43, an naɗa shi ministan kuɗi a Agustan bara kuma ya gudanar da ayyukan sauyi irin daban-daban, daga ciki har da ƙoƙrin korar ma'aikatan bogi da kuma toshe wuraren da kuɗaɗen haraji na ƙasar ke sulalewa.