Sabon shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya naɗa uban-gidansa kuma fitaccen ɗan siyasar nan da ya goyi bayansa Ousmane Sonko a matsayin firaiminista.
Sonko, wanda babban ɗan hamayya ne ga tsohon shugaban ƙasar Macky Sall, yana da matuƙar farin-jini a tsakanin matasan ƙasar, ko da yake an haramta masa tsayawa takara a zaɓen ranar 24 ga wata Maris sakamakon zargin ɓata suna. Sai dai ya musanta wannan zargi.
"An naɗa Ousmane Sonko a matsayin firaminista," a cewar Oumar Samba Ba, babban sakatare a fadar shugaban ƙasa, a yayin da yake jawabi a gidan talbijin na ƙasar wato RTS.
Sonko, mai shekara 49, ya kwashe shekaru biyu yana kai ruwa rana da tsohuwar gwamnatin kasar, lamarin da ya kai ga yin jerin zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Daga bisani an haramta masa tsayawa takara amma ya buƙaci magoya bayansa su goyi bayan Faye a zaɓen shugaban ƙasar.
'Diomaye da Sonko ɗaya suke'
Mutanen biyu sun yi yaƙin neman zaɓe mai taken "Diomaye is Sonko," wato Sonko 'Diomaye da Sonko ɗaya suke' inda Sonko ya riƙa kira ga magoya bayansa su zaɓi Faye, wanda ya lashe zaɓen da fiye da kashi 54 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Faye ya sha rantsuwar kama aiki ranar Talata inda ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a ƙasar.
Da yake magana bayan naɗa shi a matsayin firaiminista, Sonko ya ce zai miƙa wa shugaban ƙasa Faye jerin sunayen mutanen da za a bai wa muƙaman ministoci domin ya amince da su.
"Ba za mu bar (Faye) shi kaɗai ya ɗauki wannan babban nauyi ba", in ji Sonko.