Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ce 'yan hamayya da suka mamaye majalisar sun sa yana shan wahala wajen gudanar da "sauye-sauye masu ma'ana." /Hoto: Reuters

Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya rusa majalisar dokokin ƙasar da ke ƙarkashin jagorancin 'yan adawa a ranar Alhamis, a wani yunkuri na kawo ƙarshen rashin jituwar dake tsakanin majalisar da ɓangaren zartarwa.

A wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasa, Faye ya ce za a gudanar da zaɓen gaggawa a ranar 17 ga watan Nuwamba na bana.

Ya ce “dogaro da ikon da sashi na 87 na Kundin Tsarin Mulki ya ba ni, kuma bayan tuntuɓar Majalisar Tsarin Mulki a kan ranar da ta dace, da tuntuɓar Firayiminista da Shugaban Majalisar Dokoki, na rushe Majalisar Dokoki ta ƙasa.”

Matakin ya zo ne watanni shida bayan da aka zabi Faye a ƙarkashin jam'iyyar adawa.

'Sauye-sauye masu ma’ana'

Ya ce rinjiyen da ‘yan hamayya ke da shi a majalisar ya sa yana shan wahala wajen aiwatar da “sauye-sauye masu ma’ana” da ya yi alkawari a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya roƙi masu kaɗa ƙuri’a da su zaɓi 'yan jam’iyyarsa ta Patriots of Senegal for Work, Ethics and Fraternity (PASTEF).

Mambobin ƙawancen tsohon Shugaban Ƙasar Macky Sall na Benno Bokk Yakaar (United in Hope) su ne suke da rinjaye a majalisar mai barin gado wacce aka zaɓa a shekarar 2022.

A baya-bayan nan dai an samu takun saƙa tsakanin aɓngaren zartarwa da na majalisar bayan da ‘yan majalisar hamayya suka soke muhawara kan kasafin kuɗi tare da yin barazanar gabatar da ƙudirin tace ayyukan gwamnati.

'Cibiyoyin da suke murɗa al’amura'

Ƙungiyar ‘yan majalisar Benno Bokk Yakaar ta soki matakin rusa majalisar, inda ta ce an yi shi ne da nufin kauce wa gabatar da ƙudirin tace ayyukan gwamnati da ‘yan majalisar masu rinjaye za su yi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta zargi Shugaba Faye da Firayiminista Ousmane Sonko da “yin amfani da cibiyoyi don biyan buƙatun kansu na siyasa.

Abdou Mbow, shugaban ƙungiyar masu rinjaye a majalisar ya ce "Wannan rusa majsaliar wani yunkuri ne ƙarara na rufe bakin 'yan hamayya a majalisar, da kuma kauce wa duk wata muhawara ta dimokradiyya kan yadda ake tafiyar da ƙasar.

TRT Afrika