Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya naɗa ministoci ranar Juma'a, waɗanda yawancinsu sabbin-jini makonni kaɗan bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar.
Faye, mai shekara 44, wanda bai taɓa riƙe wani muƙami na siyasa kafin ya zama shugaban ƙasa ba, ya samu gagarumar nasara a zagaye na farko na zaɓen, abin da ya sa ya zama shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a tarihin Senegal.
Da alama Faye yana so ya raba ɗaunin iko ne da uban gidansa na siyasa kuma fitaccen ɗan siyasa Ousmane Sonko, wanda ya bai wa muƙamin firaiministan bayan ya taimaka masa wurin lashe zaɓen.
Sonko ya sanar da sunayen mutum 25 da ya bai wa muƙaman ministoci ranar Juma'a, inda ya ce za su gudanar da ayyuka daban da yadda aka saba yi a baya.
Man fetur da iskar gas
"Wannan gwamnati da aka kafa ranar 5 ga watan Afrilu ta musamman ce... za ta aiwatar da ayyukan da al'ummar Senegal suka zaɓe ta domin ta yi," in ji Sonko.
Sonko, mai shekara 49, ya jagoranci gwagwarmayar kawo sauyi a Senegal amma an hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa kan zarge-zargen da aka yi masa na ɓata tarbiyyar matasa, abin da ya sa ya goyi bayan Faye wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.
An naɗa Birame Souleye Diop a matsayin minista makamashi, muƙami mai muhimmancin gaske ganin cewa a 2024 ƙasar za ta soma samar da man fetur da iskar gas.
Haka kuma an naɗa Ousmane Diagne a matsayin ministan shari'a. Ya taɓa riƙe muƙamin mai shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta birnin Dakar.
Samar da ayyuka
A cikin ministocin akwai mata huɗu waɗanda aka naɗa a muƙaman ministan harkokin wajen da kamun kifi da iyali, da matasa da al'adu
Senegal na fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da rashin aikin yi wanda ya kai kashi 20 cikin ɗari.
Sonko ya ce gwamnatinsu za ta mayar da hankali wurin bai wa matasa aiki da rage farashin kayayyaki da kare ƴancin ɗan'adam.