Janar din sojan, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, ya jagoranci juyin mulkin da ba a zubar da jini ba na hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba ranar 30 ga watan Agusta. Hoto: TRT AFRIKA

Sabon shugaban mulkin sojin Gabon Janar Brice Oligui Nguema ya nada tsofaffin shugabannin adawa da ma na hannun-damar hambararren shugaban kasar a matsayin mambobin majalisar dokoki.

Janar din sojan, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, ya jagoranci juyin mulkin da ba a zubar da jini ba na hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba ranar 30 ga watan Agusta.

Sa'o'i kadan kafin hakan, an ayyana Bongo wanda zuri'ar gidansu ta shafe shekara 55 tana mulkin kasar, a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a makon, wanda sojojin suka ce cike yake da magudi.

Oligui ya yi alkawarin mika mulkin kasar ga farar-hula ta hanyar gudanar da zabe bayan gwamnatin rikon kwaryar, amma bai fadi ranar yin hakan ba.

Ya kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin wani sabon firaiminista Raymond Ndong Sima, wani dan kasar mazaunin Paris kuma masanin tattalin arziki, wanda ya taba rike mukamin firaiminista a karkashin Bongo daga shekarar 2012 zuwa 2014, amma daga bisani ya tsaya takara tare da shi a 2016 da 2023.

Paulette Missambo ne zai jagoranci majalisar dattijan kasar, wanda babban mai hamayya ne da Bongo a zaben da aka yi, kuma shi ne shugaban Jam'iyyar National Union, ya karanto dokar da Oligui ya sanya a wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin na gwamnatin kasar.

Jean-Francois Ndongou, wanda ya taba rike mukaman minista a lokuta da dama a zamanin mulkin zuri'ar gidan Bongo, shi ne zai zama shugaban Majalisar Wakilan kasar.

Kazalika akwai tsofaffin mataimakan shugaban kasa hudu — da jami'an soji da 'yan siyasar da suka yi adawa da Bongo da ma jami'an kungiyoyin fararen-hula - duk a cikin mambobin majalisar.

Ana kuma sa ran Oligui zai nada mambobi 70 na majalisar wakilan da kuma 50 na majalisar dattijai.

Sabon kundin tsarin mulki

Sabuwar gwamnatin wacce Ndong Sima ya sanar a ranar Asabar ta kunshi jami'an soji da tsofaffin ministocin da suka yi aiki a karkashin shugabancin Ali Bongo Ondimba.

Oligui ya yi alkawarin samar da sabon kundin tsarin mulki wanda za a amince da shi a bisa tsarin kuri'ar raba gardama da kuma samar da sabuwar dokar zabe.

Sannan kuma a ranar Litinin an rage tsawon sa'o'in dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin Bongo ta saka gabanin sanar da sakamakon zabe wacce sojojin suka kara tabbatar da ita a birnin Libreville da kewayansa da awa hudu, inda a yanzu take aiki daga tsakanin karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Amma dokar takaita zirga-zirgar za ta ci gaba daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a sauran sassan kasar, kamar yadda mulkin sojin ya sanar.

AFP