Shugaba Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin mai ba da shawara kan tsaro

Shugaba Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin mai ba da shawara kan tsaro

Nuhu Ribadu shi ne shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya na farko.
Ribadu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman kan sha'anin tsaro.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis.

Baya ga Nuhu Ribdado, shugaban kasar ya yi wasu karin nade-naden na masu ba shi shawara na musamman kan al'amura dabam-dabam.

Kazalika Shugaba Tinubu ya nada Mr. Dele Alake a matsayin mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare, yayin da ya nada Mr. Yau Darazo a matsayin mataimaki na musamman kan siyasa da hulda da gwamnatoci.

Sauran mutanen da ya nada sun hada da:

  • Mr. Wale Edun - Mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kudi
  • Mrs. Olu Verheijen - Mai ba da shawara ta musamman kan Makamashi
  • Mr. Zachaeus Adedeji - Mai ba da shawara na musamman kan Kudaden Shiga
  • Mr. John Ugochukwu Uwajumogu - Mai ba da shawara na musamman kan Masana'antu da Kasuwanci da Zuba Jari
  • Dr (Mrs.) Salma Ibrahim Anas - Mai ba da shawara na musamman kan Harkar Lafiya.

Nuhu Ribadu shi ne shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya na farko.

Ya shugabancin hukumar daga shekarar 2003 zuwa 2007, a lokacin mulkin Shugaba Obasanjo.

Ya kuma taba yin takarar shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam'iyyar ACN wadda Tinubu ya taba jagoranta a shekarar 2011.

A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya fara nade-nade inda ya nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa da Sakataren Gwamnatin Tarayya.

TRT Afrika