A shekarar 2020 ne Assimi Goita ya hau karagar mulki bayan kifar da shugaban lokacin Ibrahim Boubacar Keita.

Shugaban mulkin soji na Mali ya ƙara wa kansa girma zuwa mukamin Janar da matsayi na musamman: Kanar Assimi Goita na rundunar sojin ƙasa - muƙamin soji mai girma da shugabanni biyu na ƙasar ne suka taɓa riƙe shi a tarihin Mali.

Wannan mataki na zuwa ne shekara guda bayan da gwamnatin Mali ta amince da sabon kundin tsarin mulki da ya ƙara ƙarfin shugaban ƙasa da rundunar soji.

Majalisar Ministoci ce ta fitar da sanarwar a ranar Laraba, wadda aka buga a shafin intanet na gwamnatin Mali.

Kazalika, an ƙara wa wasu masu muƙamin kanar su biyar matsayi zuwa cikakkun Janar masu tauraro huɗu.

A 'yan shekarun nan Mali ta fuskanci juyin mulkin soji sau biyu, a watan Agustan 2020 da Mayun 2021.

TRT Afrika